'Dole Tinubu Ya Zarce,' Minista Ya Bukaci 'Yan APC Su Tashi Tsaye kan 2027
- Ministan Sufurin Jiragen Sama ya ce dole ne ‘yan APC su fifita zarcewar Bola Tinubu a 2027 ko da hakan zai iya yi wa siyasar su illa
- Ya ce idan wani sabon shugaban kasa ya hau mulki a 2027, hakan na iya rushe gyare-gyaren da Tinubu ya fara tun da ya shiga ofis a 2023
- Festus Keyamo ya sadaukar da shugabancin jam’iyya a jihar Delta ga Gwamna Sheriff Oborevwori domin ƙarfafa APC da haɗa kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya shawarci mambobin jam’iyyar APC su mayar da hankali kan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Ya ce wannan ne kadai zai bawa Tinubu damar kammala muhimman gyare-gyaren da ya soma a tsarin mulki da tattalin arziki.

Asali: Twitter
Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels TV a shirin Politics Today da aka gabatar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo ya bayyana cewa tazarcen Tinubu ya fi kowace bukata muhimmanci a halin yanzu, ko da hakan zai iya shafar muradin wasu ‘yan siyasa a APC.
Ya ce kamata ya yi kowa ya sadaukar da kansa domin ci gaban jam’iyya da kuma ci gaban kasa baki ɗaya.
Festus Keyamo ya jaddada cewa Tinubu yana bukatar wa’adi na biyu domin tabbatar da nasarar tsare-tsaren da ya fara aiwatarwa.
Keyamo ya ce Tinubu na bukatar tazarce
Keyamo ya ce zai zama babban rashi idan wata sabuwar gwamnati ta hau a 2027 ta rushe duk wani tsari da Tinubu ya soma.
Ya ce hakan ne ya taba faruwa a shekarun baya lokacin da ake sauya gwamnatoci ba tare da dorewar manufofi ba.
Ministan ya ce:
“Ya kamata kowane ɗan APC ya maida hankali kan nasarar Tinubu. Ko da kuwa hakan zai shafi sha’anin siyasar mutum, muhimmin abu shi ne dorewar gyare-gyaren da aka soma.”
Ministan ya bayyana cewa zarcewar Tinubu a 2027 ce kadai za ta bai wa Najeriya damar kammala manufofin sauyi da aka riga aka fara, musamman a bangaren tattalin arziki da tsaro.
Maganar shugabancin APC a jihar Delta
Keyamo ya ce ya mika shugabancin APC a jihar Delta ga Gwamna Sheriff Oborevwori, wanda ya sauya sheka kwanan nan daga jam’iyyar PDP.
A cewar ministan:
“Ko da hakan yana nufin zan rasa dama a siyasa, hakan bai dame ni ba. Abin da yafi muhimmanci shi ne Shugaba Tinubu ya ci gaba da mulki domin al’umma su amfana.”

Asali: Facebook
Keyamo ya ce PDP ta rushe a jihar Delta
Keyamo ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta rushe a jihar Delta bayan sauya shekar Gwamna Oborevwori zuwa APC, yana mai cewa hakan babbar nasara ce ga APC a Kudu maso Kudu.
Daily Post ta wallafa cewa Keyamo ya ce:
“Delta ce ke ɗaukar nauyin PDP tun da, kuma ita ce ginshiƙin jam’iyyar. Yanzu da Gwamna ya dawo APC, PDP ta rasa madogara,”
Delta: Dalilin Okowa na komawa APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya yi bayani kan dalilin komawar shi APC daga jam'iyyar PDP.
Okowa ya ce samun sauyi a siyasa domin cimma wata manufa mai kyau ba sabon abu ba ne kuma sauya shekar za ta kawo nasara ga jihar Delta.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa ya shafe shekaru takwas yana adawa a lokacin shi, wanda hakan ya kawo wa jihar koma baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng