El Rufa'i Ya Gano Wanda Ya Fi Dacewa Ya Mulki Najeriya a 2027

El Rufa'i Ya Gano Wanda Ya Fi Dacewa Ya Mulki Najeriya a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Najeriya tana bukatar shugaba mai hangen nesa domin a ceto 'yan kasa
  • Ya ce matsalolin da kasar ke fuskanta sun yi tsanani fiye da a ci gaba da rikon tsarin karba-karba a tsakanin shiyyoyin kasar nan
  • El-Rufai ya shawarci matasa da su kaurace wa karaya da fushi maras amfani, su mayar da hankalinsu wajen gina kasa da nema wa kansu mafita
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa akwai kokarin hade kungiyoyin siyasa guda biyar domin kafa sabuwar hadin guiwa a karkashin SDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sauya ra'ayi a kan tsarin karba karba a tsayin mulkin Najeriya.

Ya bayyana cewa cancanta, ba yankin da dan takara ya fito ba, shi abin da ya kamata ya zama tushen zaben shugabannin Najeriya na gaba.

Nasir
Nasir El-Rufa'i ya ce cancanta ake nema ba yankin dan takara ba Hoto: King SLS II– The Legend
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa El-Rufa'i ya yi wannan bayani ne bayan ziyarar da ya kai ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da kuma tattaunawa da shugabannin jam'iyyarsa, SDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dalilin da ya sa na bar APC,' El-Rufa'i

Daily Post ta wallafa cewa El-Rufa'i ya kare matakin da ya dauka na sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP a kwanakin baya.

Ya ce ya dauki matakin ne da nufin taimakawa wajen gina wata sahihiyar dandalin siyasa a lokacin da jama'a ke fuskantar rashin jin dadin jam'iyyun da ke akwai.

Ya ce:

"Shekaru na 65, na yi wa Najeriya hidima a matsayin minista da gwamna. Zan iya yin ritaya, amma na yi imanin kasar tana fuskantar wani babban kalubale wanda ke bukatar agajin gaggawa."

Tsohon gwamnan ya musanta zargin cewa barin APC ne saboda ya gaza samun biyan bukatarsa ta kashin kai daga gwamnatin Bola Tinubu.

El-Rufai ya yi kira ga matasa

El-Rufai ya yi kira ga matasan Najeriya da cewa kar su karaya, sai dai za su iya mayar da damuwarsu hanyar gina kyakkyawar makoma.

Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ya ce:

"Kowane yaro na Najeriya yana da hakkin samun damar da na samu. Ba za mu bar wannan kasar a hannun shugabannin da ke cike da rashawa ba."

Ya kuma bayyana cewa akwai tattaunawa tsakanin manyan kungiyoyi na siyasa guda biyar domin gina wata hadaka mai karfin adawa a karkashin jam'iyyar SDP.

Ficewar El-Rufai daga APC zuwa SDP

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bar jam’iyyar APC ya koma SDP, domin kafa sabON dandalin siyasa da zai kawo sauyi a Najeriya.

A cewarsa, Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma ba lokaci bane na karba-karba tsakanin yankuna, sai dai cancanta da hangen nesa.

Ya ce kasar na bukatar shugaba mai tsari da gaskiya, wanda zai fitar da ita daga halin da take ciki.

El-Rufai ya bayyana cewa yana kokarin hada kungiyoyin siyasa guda biyar domin kafa sabuwar hadaka a karkashin SDP.

Wannan hadin gwiwar na nuni da yunkurin kafa sabuwar babbar jam’iyya da za ta iya kalubalantar APC da PDP a zaben 2027.

Ya musanta rade-radin cewa ya bar APC ne saboda rashin samun wata bukata ta kashin kansa daga gwamnatin Tinubu.

A ganinsa, matasa ne ke da makomar kasar, don haka ya yi kira gare su da su guji fushi da kauracewa siyasa, su shiga domin canza al’amura.

El-Rufai na iya zama gwarzon kafa sabuwar tafiya ko kuma ya tsaya takara idan bukatar hakan ta taso. Yunkurinsa na nuna kishin kasa da neman mafita ga matsalolin Najeriya.

'El-Rufa'i zai yiwa zaben Tinubu illa,' Masani

A baya, mun wallafa cewa masanin siyasa kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, Majeed Dahiru, ya yi magana kan yadda za a iya kawo ƙarshen mulkin Bola Tinubu a 2027.

Dahiru ya bayyana cewa nasarar Nasir El-Rufai wajen haɗa kan manyan ƴan siyasar Arewa zai iya zama babban makamin da zai kawo ƙarshen mulkin Shugaba Tinubu.

Majeed Dahiru ya ba da shawara ga El-Rufai kan yadda zai taka muhimmiyar rawa a cikin zaben 2027 ta hanyar haɗe kan manyan yan siyasa, musamman na Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.