Yarabawa Sun Nemi Kwanwaso Ya Hada kai da Tinubu, Ya Bar Atiku da El Rufa'i

Yarabawa Sun Nemi Kwanwaso Ya Hada kai da Tinubu, Ya Bar Atiku da El Rufa'i

  • Wata kungiyar matasan Yarabawa ta roki Rabiu Musa Kwankwaso da ya watsar da kiran shiga hadakar da ake shiryawa domin kifar da Bola Tinubu
  • Shugaban kungiyar, Hammer Olalekan, ya bayyana cewa hadakar da ake kokarin kafa wa ba ta da karfin da za ta iya kada APC daga mulkin Najeriya
  • Matasan kungiyar sun yi ikirarin cewa ko Kwankwaso bai shiga APC ba, Bola Tinubu zai sake lashe zabe a 2027 saboda kwarewarsa a harkar siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar matasan Yarabawa ta (YYSA) ta bukaci tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya yi watsi da kiran da ake yi masa na shiga hadaka a 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu shugabannin siyasa ke kokarin hada kawunansu don hana Bola Tinubu samun wa’adi na biyu idan ya tsaya.

Tinubu
Kungiyar YYSA ta bukaci Kwankwaso ya yi watsi da maganar hadaka a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Leadership ta rahoto cewa shugaban kungiyar, Hammer Olalekan ne ya fadi haka a ranar Lahadi a Ibadan, inda ya ce Kwankwaso babban dan siyasa ne da bai dace ya zauna a adawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olalekan ya kara da cewa tsarin da ake kokarin yi ba shi da karfi kamar yadda aka yi a shekarar 2015 lokacin da aka hada jam'iyyu da dama domin kifar da Goodluck Jonathan.

'Hadaka ba za ta yi tasiri ba,' YYSA

Shugaban matasan ya bayyana cewa hadakar da ake kokarin kafa wa yanzu ba ta da irin karfi da kwarjinin wacce ta fitar da Goodluck Jonathan daga ofis.

A cewarsa, hadakar da ta yi nasara a 2015 ta kunshi gwamnoni da dama daga Arewa da Kudu da kuma jam'iyyu da dama kamar ACN, CPC, tsagin PDP, LP da wani bangare na APGA.

Ya ce sabuwar hadakar da ake kokarin kirkirowa karkashin Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai ba ta da karfi, kuma ba za ta iya kada APC a zaben 2027 ba.

YYSA: Tinubu zai ci zabe ko babu Kwankwaso

Olalekan ya jaddada cewa, ko da Kwankwaso bai shiga APC ba, Bola Ahmed Tinubu zai sake samun nasarar lashe zaben 2027 saboda kwarewarsa a harkokin siyasa.

Ya bayyana Tinubu a matsayin gogaggen dan siyasa wanda ya san dabarun samun nasara fiye da yawancin ‘yan adawa.

Kungiyar ta shawarci Kwankwaso da ya yi la’akari da yiwuwar komawa APC maimakon shiga hadakar ‘yan adawa domin ciyar da kansa da muradunsa gaba.

YYSA ta ce Kwankwaso na da kwarjini da tasiri

Shugaban matasan ya bayyana Kwankwaso a matsayin babban dan siyasa mai tasiri wanda ya kamata a rika yin la'akari da matsayinsa a harkokin siyasa.

The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta yi fatan ganin Kwankwaso ya dauki matakin da zai fi masa amfani a siyasarsa da makomar dimokuradiyya a Najeriya.

Kwankwaso
An bukaci Kwankwaso ya shiga APC maimakon hadaka da 'yan adawa. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Kwankwaso ya hadu da El-Rufa'i a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya hadu da Malam Nasir El-Rufa'i a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa manyan jagororin adawar sun hadu ne a wani masallaci a ranar Juma'ar da ta wuce.

Lamarin ya kara jawo ce-ce-ku-ce a harkokin siyasar Najeriya, musamman ganin yadda 'yan adawa ke maganar hadaka a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng