Abokin Takarar Atiku a 2023 Ya Fadawa Shettima, Ganduje Dalilin Komawar Shi APC
- Tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, da gwamna mai ci, Sheriff Oborevwori, sun bayyana dalilin sauya sheƙarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC
- Ifeanyi Okowa ya ce sun ɗauki matakin ne domin kawo cigaba a jihar Delta da al’ummarta, musamman wajen haɗa kai da gwamnatin tarayya
- Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa hakan zai ba jihar damar amfana da albarkatun kasa da goyon bayan d ake samu a birnin Abuja domin gina Delta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - A wani babban biki da aka gudanar a filin taro na Cenotaph da ke Asaba, tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana dalilin sauya sheƙarsu daga PDP zuwa APC.
Okowa, tare da gwamna Sheriff Oborevwori da sauran jiga-jigan PDP a jihar, sun sanar da sauya sheƙarsu a cikin makon da ya gabata.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta rawaito cewa Okowa ya bayyana cewa matakin da suka ɗauka na da nufin tabbatar da moriya wa jama'ar jihar Delta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da ya sa su Okawa sauya sheka
Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa mutane da dama sun yi mamakin sauya shekar da suka yi, amma sun yanke shawarar ne domin kawo alheri da cigaban jihar.
Ya ce tarihi ya nuna cewa a wasu lokuta sai an sauya hanya domin samar da abu mafi alheri ga jama'a, kuma wannan sauyi wani yunƙuri ne na haɗa kai da gwamnatin tarayya.
Bukatar hada kai da gwamnatin tarayya
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a zamaninsa da ya shafe shekara takwas a cikin adawa, jihar ta rasa abubuwa masu yawa da za ta iya samu daga gwamnatin tarayya.
Ya ce domin kaucewa irin wannan koma baya ga gwamna mai ci, dole ne su haɗa kai da babban tushen albarkatu da ikon siyasa da ke Abuja.
Ifeanyi Okowa ya bayyana haka ne a gaban jiga jigan APC da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

Asali: Twitter
Maganar karfafa APC a jihar Delta
Rahoton Channels TV ya nuna cewa Okowa ya ce matakin da suka ɗauka yana da matuƙar muhimmanci kuma zai ƙarfafa jam’iyyar APC a jihar Delta.
Ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a haɗa kai tsakanin tsofaffin ‘yan APC da masu sauya sheƙa domin samun nasarar jam’iyyar a jihar.
Bugu da kari, ya kuma bayyana cewa suna goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamna Oborevwori domin cimma nasara a faɗin jihar Delta da ma ƙasa baki ɗaya.
An bukaci Kwankwaso ya shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar matasan Yarabawa ta yi kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga APC.
Shugaban kungiyar ya ce bai kamata gogaggen dan siyasa kamar Sanata Kwankwaso ya zauna a jam'iyyar adawa ba, musamman lura da yadda yake da tasiri a siyasa.
Legit ta rahoto cewa kungiyar ta bukaci Kwankwaso ya yi watsi da maganar hadaka da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufa'i ke kokarin samarwa.
Asali: Legit.ng