2027: Tsohon Shugaban PDP Ya Fadi babbar Matsala 1 da Tinubu, APC Za Su Fuskanta

2027: Tsohon Shugaban PDP Ya Fadi babbar Matsala 1 da Tinubu, APC Za Su Fuskanta

  • Tsohon mataimakin shugaban PDP, Chief Olabode George, ya tabbatar cewa Najeriya ba za ta zama ƙasa mai tsarin jam’iyya ɗaya ba
  • A cewarsa, taron NEC na PDP zai tantance makomar jam’iyyar, tare da fitar da hanyoyin farfado da ita daga rikice-rikicen cikin gida
  • George ya soki masu sauya sheƙa zuwa APC, yana mai cewa 'yan Najeriya sun waye, kuma za su ƙi jam’iyya mara aƙida da nagarta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Chief Olabode George, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta zama ƙasa mai tsarin jam’iyya ɗaya ba.

George ya bayyana kwarin gwiwa kan jam'iyyar PDP duk da yawaitar sauya shekar da ke faruwa a kwanan nan gabanin zaɓen 2027.

Bode George ya ce 'yan Najeriya sun waye, ba za su yarda da tsarin jam'iyya 1 ba.
Hagu zuwa Dama: Bode George, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Bode George ya fadi matsalolin gwamnatin APC

A hirarsa da Vanguard, Bode George ya ce PDP za ta tantance makomarta da sanin hanyar farfadowarta daga rikice-rikicen da suka dabaibaiyeta a taron NEC mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Game da makomar PDP, George ya nuna cewa ana kururuta gwamnatin APC ne kawai, amma ba inda za ta ce, yana mai tambayar:

“Me suka gani da ya sa suke son dawo da Shugaba Bola Tinubu a 2027? Babu! Domin tattalin arziki ya tabarbare.
"Akwai rashin tsaro, yawaitar garkuwa da mutane da kashe-kashe, sannan babu wani ci gaba da aka samu na magance wadannan matsalolin."

Da wannan ne, tsohon jagora a babbar jam'iyyar adawa ta kasar yake ganin 'yan Najeriya ba za su sake amince da zaben gwamnatin APC ba.

"Ba za a yarda da jam'iyya 1 ba" - George

Bode George ya soki masu sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, yana mai cewa suna barin jam’iyya mai tsari zuwa wadda ba ta da aƙida.

Ya bayyana cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya bar PDP saboda tasirin Ifeanyi Okowa, wanda ya dauke shi matsayin ubangidansa.

George ya ce Najeriya ba za ta zama ƙasar da ke tafiya a tsarin jam’iyya ɗaya ba, domin ’yan Najeriya sun waye kuma za su tsaya kan gaskiya.

Ya bayyana cewa mulkin jam’iyya ɗaya ba zai yiwu a Najeriya ba saboda ƙasar tana da kabilu daban-daban kuma ba mulkin soja ake yi ba.

A cewarsa, kowane shugaban kasa yana da shekaru huɗu ko takwas kawai, daga nan dole ya bar ofis, ba wai zai dawwama ba ne a kan mulki.

Bode George ya ce PDP za ta san makomarta a zaben 2027 ne yayin zaben NEC na gaba
Bode George, tsohon mataimakin jam'iyyar PDP na kasa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Bode George ya fadi makomar PDP gabanin 2027

Game da matakan da jam'iyyar PDP za ta dauka, George ya ce:

"Taron kwamitin zartarwar jam'iyya (NEC) ne zai bayyana ko PDP za ta ceci kanta ko za ta saduda ta durkushe har zuwa kasa."

Ya bayyana cewa bayan taron NEC ne za a tantance sahihan 'yan demokuradiyya da ke da kishin jam'iyyar PDP.

Game da bambance-bambancen Arewa da Kudu, George ya ce, "Najeriya ƙasa ce guda ɗaya, ba wani bambancin Arewa da Kudu.

"Kowane ɗan Najeriya yana da muhimmanci. Matsayinmu na dattawa shi ne kare gaskiya da adalci da kuma hango abin da zai iya zuwa ya dawo."

George ya jaddada cewa ba ya jin tsoron faɗa wa duk wani shugaba gaskiya, domin hakan shi ne amana ga kasa.

Bugaji ya fallasa dabarar APC gabanin 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ɗan majalisa, Usman Bugaje, ya zargi jam’iyyar APC da amfani da kuɗi wajen rinjayar manyan ‘yan PDP su sauya sheka zuwa cikinta.

Bugaje ya bayyana cewa amfani da kuɗi ko barazana wajen tilasta sauya sheka yana haifar da barazana ga ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya kuma soki PDP kan martanin ta a sauya shekar gwamnan Delta, yana mai cewa jam’iyyar ta nuna rauni da gazawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.