Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Zarra a Afrika, Ta Samu Babbar Lambar Yabo

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Zarra a Afrika, Ta Samu Babbar Lambar Yabo

  • Rundunar Sojin Najeriya ta samu lambar yabo daga African Security Watch a matsayin mafi ƙwarewa a Afirka wajen yaƙi da ta'addanci a 2025
  • Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sadaukar da lambar yabon ga sojojin da suka rasa rayukansu da iyalansu
  • Kungiyar African Security Watch ta ce nasarorin rundunar sun samo asali ne daga haɗin gwiwa, tattara bayanan sirri da inganta horon sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja – Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta samu wata babbar nasara a matakin nahiyar Afirka bayan an karrama ta a matsayin rundunar soja mafi ƙwarewa wajen yaƙi da ta'addanci a shekarar 2025.

Ƙungiyar African Security Watch ce ta ba rundunar wannan lambar yabo saboda irin nasarorin da ta samu a ayyukan yaƙi da ta'addanci, jagoranci da kuma gudunmawar da take bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a Najeriya da yankin Afirka.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP ya fallasa gwamnati, ya fadi abin da ya jawo lalacewar tsaron Najeriya

An karramar rundunar sojojin Najeriya da lambar yabo ta mafi kwarewa a Afrika
An miƙa lambar yabo ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a hedikwatar rundunar da ke Abuja. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An miƙa lambar yabo gaundunar sojin ƙasa

Kanal Appolonia Anele, mukaddashiyar darakar hulda da jama'a ta rundunar sojojin kasa ta sanar da hakan a sanarwar da ta fitar kuma aka wallafa a shafin rundunar na X a ranar 29 ga Julin 2026

An miƙa lambar yabon ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a hedikwatar rundunar da ke Abuja ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2026.

Babban Janar Teriworie Gagariga ne ya gabatar da lambar bayan ya karɓe ta a madadin rundunar sojin Najeriya a bikin bada lambar yabo ta African Security Watch da aka gudanar a Banjul, ƙasar Gambiya.

Da yake karɓar lambar yabon, Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa wannan karramawa ta nuna jarumtaka, ƙwarewa da jajircewar jami'ai da dakarun rundunar sojin Najeriya.

Rundunar za ta ƙara ƙarfafa yaƙi da ta'addanci

Ya sadaukar da lambar yabon ga sojojin da suka rasa rayukansu yayin kare ƙasar, tare da yabawa iyalansu kan irin goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan yaran da ake ba horo kan jirage marasa matuka

Babban hafsan ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, horas da jami'ai, inganta walwalar sojoji da kuma samar da sabbin kayan aiki.

Ya ce manufarsa ita ce gina rundunar soja mai ƙwarewa, shirye-shiryen yaƙi da kuma iya fuskantar sabbin barazanar tsaro a Najeriya da yankin Afirka.

An karrama rundunar sojojin kasan Najeriya.
An miƙa lambar yabo ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a hedikwatar rundunar da ke Abuja. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Dalilan da suka sa rundunar ta samu karramawar

A cewar African Security Watch, rundunar sojin Najeriya ta cancanci wannan karramawa ne saboda nasarorin da ta samu a ayyukan haɗin gwiwa, amfani da bayanan sirri wajen gudanar da hare-hare, kyakkyawar hulɗa da fararen hula da kuma bunƙasa ƙarfin rundunar.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa rundunar sojin Najeriya ta zama abin koyi ga sauran rundunonin soji a Afirka wajen yaƙi da ta'addanci da ƙarfafa tsaron yankin.

Rundunar soji ta nada sababbin kwamandojoji

A wani labari, mun ruwaito cewa, Babban Hafsan Sojin Kasa ya amince da nada sabbin manyan kwamandoji bayan gwamnatin Tinubu ta amince da kirkirar rundunonin soja guda hudu.

Sabbin rundunonin za su fara aiki nan take domin fadada ayyukan soja, inganta tsaro da kuma kara karfin mayar da martani kan barazanar tsaro.

Sabon tsarin ya sake raba yankunan da rundunonin soja za su kula da su a fadin Najeriya domin inganta jagoranci da gudanar da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com