Zaben Bayelsa: Hadimin Gwamna Diri da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar APC

Zaben Bayelsa: Hadimin Gwamna Diri da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar APC

  • Hadiman gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa 2 da wasu ƙusoshin siyasa sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ƙarshen mako
  • Ɗan takarar mataimakin gwamnan APC a zaben Bayelsa da ke tafe, Joshua Maciver, shi ne ya tarbe su a gangamin ceto Sagbama
  • INEC ta zaɓi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 domin gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bayelsa - Mataimaki na musamman ga gwamna Douye Diri na jihar Beyelsa, Mista Doubara Benjamin, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

Benjamin, ya koma APC ne tare da jigon PDP mai tattara magoya baya tun daga tushe, Bodmas Prince Kemepadei, wanda ya yi murabus daga matsayin kakakin gwamna Diri.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Zaben Bayelsa: Hadimin Gwamna Diri da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar APC Hoto: Vanguardngr
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto cewa jiga-jigan biyu sun sauya sheƙa tare da ɗumbin jiga-jigan siyasa, wanda suka ƙunshi shugaban LP na gundumar Sagbama 11, Diepriye Apelebiri da sauransu.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Jam'iyyar APC Da Korar Jiga-Jigai 84

Masu sauya sheƙar sun tabbatar da matakin da suka ɗauka ne a wurin wani gangami da aka yi wa taken, "Mu tashi tsaye Sagbama" wanda kakakin APC na ƙasa, Yekini Nabena, ya shirya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran ƙusoshin siyasar da suka zaɓi shiga APC sun haɗa da Gideon Ogufe, tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai ritaya, tsohon shugaban matasa, Akposeye Odoni da Oweifabo Felix Ebikeme.

Gangamin, wanda ya tara jiga-jigan jam'iyyar APC, mambobi da ƙungiyoyin magoya baya, ya sa garin Sagbama ya cika maƙil ba masaka tsinke a ƙarshen mako.

Kun yi kyaun kai - Joshua

Ɗan takarar mataimakin gwamna a inuwar APC, Joshua Maciver, wanda ya karɓi masu sauya sheƙar hannu bibbiyu, ya yaba musu bisa matakin da suka ɗauka na yi wa APC aiki.

Ya tunatar da al'ummar Sagbama cewa ɗan Sagbama (Sanata Seriake Dickson) ne ya maida Diri gwamna, inda ya ce Diri bai yi wa mutanen Sagbama komai ba.

Kara karanta wannan

Bayan Hukuncin Kotun Zaɓe, Ministan Abuja Ya Tona Muhimmin Abu Game da Zaɓen Shugaban Ƙasa 2023

A rahoton The Nation, Joshua ya ce:

"A lokacin da muka zo wannan gangamin, ba mu san zamu tarbi masu sauya sheka ba. Mun yi tsammanin za mu zo ne don mu gode wa jama'a da roƙon kuri'unsu."
"Amma da muka zo nan sai muka ga ‘yan adawa da dama na ficewa daga jam’iyyarsu zuwa APC. Jam'iyyar nan zata doke kowace jam'iyya a Bayelsa."

Jigon APC Ya Bukaci Atiku, Peter Obi Su Hada Hannu Da Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma Babban jigon jam'iyya mai mulkin Najeriya ya buƙaci 'yan adawa su rungumi hukuncin Kotu kana su haɗa hannu da Tinubu.

Mista Williams Dakwom, mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar Plateau , ya yaba da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262