Matasa Sun Yi Babban Rashi, An Sanar da Rasuwar Hadimin Gwamna Abba a Kano

Matasa Sun Yi Babban Rashi, An Sanar da Rasuwar Hadimin Gwamna Abba a Kano

  • Wani babban rashi ya girgiza gwamnatin Kano bayan rasuwar Abdullahi Salisu Furfura, mai taimaka wa Abba Kabir Yusuf
  • Abin takaici, rahotanni sun nuna bai wuce awa guda da wallafa sako a shafin Facebook ba kafin Allah ya karbi rayuwarsa
  • An tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana’izarsa da safe a unguwar Giginyu, ya kasance mai taimakawa a sha'anin matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana cikin alhini a Kano bayan babban rashi da gwamnatin jihar ta yi na matashi da aka bayyana da jajirtacce.

An sanar da rasuwar mai taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren sha'anin matasa, Abdullahi Salisu Furfura.

Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rasu a Kano
An tabbatar da rasuwar hadimin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Abba Kabir Yusuf, NNPP Kwankwasiyya.
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da NNPP Kwankwasiyya ta wallafa a shafin Facebook da safiyar yau Juma'a 18 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Wani hadimin Abba Kabir ya rasu

A karshen watan Maris, 2025, Legit Hausa ta ruwaito cewa an sanar da rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, babban mai taimakawa Abba Kabir Yusuf kan Rediyo.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa Galadanci ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a asibiti.

Gwamnan Kano ya bayyana marigayin a matsayin ginshiki a gwamnatinsa, ya na mai addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa hakuri.

Abba Kabir ya sake rasa hadimi a Kano

A cikin sanarwar, an bayyana tasirin marigayin da kuma irin kewarsa da al'umma da gwamnatin Kano za ta yi.

An tabbatar da cewa bai wuce sa'a guda da yin rubutu a shafinsa na Facebook ba kafin ya rasu.

Sanarwar ta ce:

"Inna Lillahi wa'inna ilaihi raji'un.
"Mun samu labarin rasuwar Hon. Abdullahi Salisu Furfura, mai taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan harkokin cigaban matasa.

"Hakika wannan babban rashi ne ga gwamnatin Kano da daukacin matasa.
"Abin takaici kuma abin mamaki, rahotanni sun bayyana cewa bai wuce awa guda da yin rubutu a shafinsa na sada zumunta ba Allah (SWT) ya karbi rayuwarsa.
An rashi a Kano na wani hadimin Abba Kabir
An tabbatar da rasuwar Abdullahi Salisu Furfura da ya kasance mai taimakawa Abba Kabir a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Yaushe aka yi jana'izar marigayin a Kano?

Rahoton ya tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayin a yau Juma'a 18 ga watan Afrilun 2025 da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Giginyu.

"Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Giginyu da ke cikin birnin Kano.
"Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, ya ba iyalansa da abokan arziki hakurin jure wannan babban rashi."

- Cewar sanarwar

Hisbah ta kama matashi kan zargin baɗala

Kun ji cewa jami'an hukumar Hisbah a Kano sun cafke wani matashi bayan an gan shi a wani bidiyo yana wani abu da akuya da ake zargi da baɗala.

Matashin, mai suna Shamsu Yakubu daga Dawakin Tofa, ya bayyana cewa ya aikata hakan ne domin samun daukaka a dandalin TikTok.

Lokacin da jami’an Hisbah suka tsare shi, ya rantse da Allah SWT cewa bai tsotsi jikin akuyar ba, sai dai ya kai bakinsa kusa ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.