2027: Tsohon Jigo a APC Ya 'Tona' Dabarar Tinubu da Shirinsa na Komawa Aso Rock
- Tsohon mataimakin sakataren yada labaran APC, Timi Frank ya zargi Bola Tinubu da haddasa rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu
- Ya yi zargin cewa shugaban kasar nan ya dauki matakin ne saboda burinsa na sake samun mulkin Najeriya a kakar zaben 2027
- Frank ya bukaci Arewa ta farka, yana mai cewa yankin shi ke fama da mafi munin matsaloli duk da taimakon da suka ba Tinubu a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin sakataren yada labaran APC, Timi Frank, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da kokarin tunzura yankin Kudu da Arewa saboda bukatarsa.
Ya ce, a wurin Tinubu, zaben 2027 tsakanin shi da yankin Arewa ne, kuma saboda hakan ne yake neman goyon bayan yankin Kudu ta hanyar dabarun da ke cike da yaudara.

Asali: Facebook
Arise News ta ruwaito cewa Frank, ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, ya gargadi yankin Arewa da Kudu da kada su bari su fada tarkon Tinubu na ci gaba da mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Frank: 'Tinubu ya na matsawa gwamnonin adawa'
This Day ta ruwaito cewa Timi Frank ya kara da cewa a gefe guda, Tinubu yana matsa lamba ga ‘yan Kudun da ba sa cikin APC, musamman gwamnonin adawa na PDP, LP da APGA.
Haka kuma, ya zargi shugaban kasa da amfani da kabilanci domin samun goyon baya, tare da barazanar ayyana dokar ta-baci a jihohin da ba su mara masa baya ba.
Ya ce:
" A wurin Tinubu, zaben 2027 tsakaninsa da Arewa ne, kuma saboda haka ne yake neman goyon bayan Kudu ta hanyar yaudara da dabaru. Ya manta cewa Arewa ce ta taimaka masa ya samu mulki a 2023.”
Tinubu: Yadda ya dace a yi zaben 2027
Frank ya kara da cewa zaben 2027 bai kamata ya zama tsakanin Arewa da Kudu ba, sai dai tsakanin ‘yan takara na gari da za su iya warware matsalolin da kasar ke fuskanta.

Asali: Facebook
Ya ce:
Najeriya na bukatar shugaban kasa wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan kasa, ba wai ‘dan takarar Arewa ko Kudu ba, ko shugaban Arewa ko shugaban Kudu ba.
“Kasarmu na fama da rabuwar kai a tsakanin kabilu. Saboda haka ba za mu iya daukar shugaba wanda ke tunzura yanki daya a kan wani saboda burinsa ba.”
Frank ya shawarci Arewa kan zaben Tinubu
Timi Frank ya ce a matsayinsa na ‘dan Kudu, bai yarda da shugaban da ke amfani da kabilanci da raba kan al’umma ba.
Ya ce:
“Ina goyon bayan shugaba wanda zai hada kan ‘yan kasa, ba wanda zai raba su ba.
“Ina ba duk wani dan Arewa da ke goyon bayan Tinubu shawarar ya sake tunani. Ya kamata su fahimci cewa Arewar da ta taimaka wa Tinubu wajen hawa mulki a 2023 ita ce ke fama da halin kakanikayi mafi muni a yau.”
Sanata Lawan ya rokawa Tinubu alfarma
A baya, mun ruwaito cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a. Sanatan ya ce yin addu’a ga shugabannin kasa, musamman shugaba Tinubu yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da hadin kai, warware matsaloli da ci gaba a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne cikin sakonsa na bikin Easter, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina nuna bambance-bambancen, su kuma ci gaba da ba shugabanni hadin kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng