PDP Ta Sake Rikicewa Yayin da Ta Dakatar da Na Hannun Daman Wike, Ta Jero Dalilai

PDP Ta Sake Rikicewa Yayin da Ta Dakatar da Na Hannun Daman Wike, Ta Jero Dalilai

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo a watan Satumba, jami'yyar PDP ta shiga rikicin siyasa na cikin gida
  • Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya dakatar da mataimakin shugabanta a yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih
  • Jam'iyyar ta ce ta dauki matakin ne kan Orbih ganin irin rawar da yake takawa wurin nakasa jam'iyyar ana daf da zaben jihar Edo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Kwamitin gudanarwa na PDP ya dakatar da mataimakin shugaban jam'iyyar a yankin Kudu maso Kudu.

Jam'iyyar ta dauki matakin ne kan Dan Orbih saboda zargin kawo tsaiko a gudanar da jam'iyyar a jihar Edo.

PDP ta dakatar da mataimakin shugabanta a Kudu maso Kudu
Jami'yyar PDP ta dakatar mataimakin shugabanta a yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih. Hoto: @OfficialPDPNig.
Asali: Twitter

Edo: Jami'yyar PDP ta dakatar da Orbih

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya barar, dan takarar gwamna ya yi murabus a Gombe, ya tura sako

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a shafinta na X a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar reshen jihar Edo na fama da rikice-rikicen cikin gida yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar.

Sakataren yada labaran jami'yyar ta kasa, Debo Ologunagba ya ce Orbih ya saba dokokim jam'iyyar kan zaben fidda gwani.

Dalilan PDP na dakatar da Orbih

Ologunagba ya ce martanin Orbih da abubuwan da ya aikata game da zaben fidda gwanin jami'yyar ya saba ka'ida.

Ya ce an kafa kwamiti mai mutane shiga karkarshin jagorancin Ambasada Taofeek Arapaja domin gudanar da bincike.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan rusa zaben fidda gwanin jami'yyar da kotu ta yi a makon da ya gabata ana daf da zaɓen gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Ana fafutukar bawa mata mukaman gwamnati, an gano minista ta kashe miliyoyi kan sayen auduga

Kotu ta rusa zaben fidda gwanin PDP

A wani labarin, kun ji cewa kotu ta dauki tsattsauran mataki kan zaben fidda gwanin PDP a jihar Edo da ke cike da matsaloli.

Kotun ta rusa zaben fidda gwanin wanda ya ba Asue Ighodalo nasara a watan Faburairun 2023 da aka gudanar a jihar.

Daga bisani jam'iyyar ta dauki matakin daukaka kara dokin kalubalantar matakin da kotun ta dauka a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.