Jerin Gwamnonin PDP 2 da Suka Bayyana Shirinsu na Goyon Bayan Tinubu a 2027
- Gwamnonin jam'iyyar PDP 2 sun fito karara sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Wannan matsaya ta gwamnonin ta zo ne a lokacin da jagororin adawa a Najeriya ke shirin ƙulla kawance domin kawar da APC a zaɓe mai zuwa
- Gwamnonin sun haɗa da Fasto Umo Eno na jihar Akwa Ibom da Rt Hon. Shetƙriff Oborevwori na jihar Delta duk daga Kudancin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A yayin da siyasar zaben 2027 ke kara daukar zafi, wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun fara bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnonin sun tabbatar da cewa za su marawa Shugaba Tinubu domin ya kammala wa'adin mulki na biyu karkashin APC duk da jam'iyyarsu ɗaya ba.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa a ƴan kwanaki kadan da suka gabata, gwamnonin PDP guda biyu sun fito karara suka bayyana cewa suna goyon bayan tazarcen Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, za su yi aiki domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne awanni 24 bayan taron da suka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
A taron, kungiyar gwamnonin PDP ta nesanta kanta daga haɗakar adawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ke jagoranta da nufin kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku gwamnonin PDP biyu da tun yanzu suka bayyana cewa suna tare da Shugaba Tinubu. Ga su kamar haka:
1. Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa Jihar Akwa Ibom na tare da Shugaba Bola Tinubu, kuma zai mara masa baya domin ya zarce wa’adin mulki na biyu a 2027.
Ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da aikin titin da ya taso daga Legos zuwa Kalaba wanda aka fara a Ikot Asua da ke ƙaramar hukumar Nsit Atai.

Asali: Twitter
Gwamna Eno ya yaba da irin kokarin gwamnatin Tinubu, musamman a fannin gine-gine da ci gaban tattalin arziki.
A rahoton Premium Times, Gwamna Eno ya ce:
“Akwa Ibom na goyon bayan Shugaba Tinubu domin ya kammala ayyukan ci gaba da ya fara. Muna godiya bisa jagoranci na adalci da fifita ci gaban kasa.”
Ya ci gaba da cewa mutanen jihar Akwa Ibom ba za su ɗauki wannan gagarumin aikin da gwamnatin Tarayya ta yi musu da wasa ba, za su saka masa a 2027.
2. Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta
Shi ma Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, ya bayyana cewa wa’adinsa da na Shugaba Tinubu zai kare a tare a shekarar 2031.
Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban ma’aikatansa, Prince Johnson Erijo, a wani taron cikar shekara 49 da haihuwa na Archbishop Godday Iboyi a Sapele.

Asali: UGC
Prince Johnson ya ce:
“Yadda Shugaba Tinubu zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas a 2031, haka Gwamna Sheriff Oborevwori ma zai gama na shi wa'adin a wannan lokaci.
Ana ganin dai wannan alama ce da ke nuna Gwamna Oborevwori na tare da Shugaba Tinubu kuma zai mara masa baya a zaɓen 2027.
Gwamnonin adawa su fito ƙarara su nuna goyon bayan ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu, alama ce da ke nuna cewa zaɓen 2027 zai zo da sababbin sauye-sauye.
Shugaba Tinubu ne ɗan takarar APC a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Farouk Aliyu ya ce APC ba ta da wani ɗan takara da ya wuce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa kamar yadda suka marawa Tinubu baya har ya samu nasara a 2023, haka za su sake goyon bayansa ya lashe zaɓen 2027 da ikon Allah.
Farouk Aliyu ya tabo batun ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai daga APC, yana mai tunawa da irin rawar da ya taka a jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng