Duk da Adawa da Gwamnatin Tinubu, 'Dan Takara Ya Fadi Illar Hadakar Atiku
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya yi fatali da hadakar jam’iyyu da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai ke jagoranta
- 'Dan siyasar bai gamsu da cancantar wadanda ke yunkurin kafa sabuwat hadakar ba, ya zargi yawancin su da rashin gaskiya da rikon amana
- Sowore ya kara da bayyana cewa babu bambanci da wacce aka hada a baya, ya ce wadanda ke kokarin kafa wannan hadaka su suka kafa APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon dan takarar shugaban kasa a AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana matsayinsa kan yunkurin kafa hadakar jam’iyyu a Najeriya kafin zaben 2027.
Ya caccaki wadanda ke jagorantar wannan yunkuri, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sowore ya yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Litinin yayin wata ganawa da manema labarai yayin bikin zagoyowar ranar haihuwar matar jigo a SDP, Adewole Adebayo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yele Sowore ya yi fatali da hadakar Atiku
Sowore ya bayyana cewa duk da yana goyon bayan hadakar jam’iyyu da kafuwar gagarumar adawa, ba zai iya marawa yunkurin da Atiku da El-Rufai ke jagoranta baya ba.
Ya ce:
“Ina maraba da hadakar jam’iyyu da adawa, amma ba irin wadda ke dauke da mutane kamar El-Rufai ba. Lokacin da a ka ba su abin da suke nema, za su koma inda suka fito.”
Sowore: 'Su Atiku ba su da cancanta'
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya yi zargin cewa yawancin ‘yan siyasar da ke cikin wannan hadaka ba su da gaskiya ko cancanta wajen jagorantar sauyi a Najeriya.
Ya ce:
“Kun manta APC ma hadaka ce? Wadanda ke son kafa sabon hadaka sun fito ne daga APC. A hakikanin gaskiya, mafi yawansu tsofaffin ministocin Buhari ne — mutanen da ya kamata su kasance a gidan yari, ba cikin wata kungiya ta hadin kai ba.”
Sowore ya bayyana cewa ba zai taba marawa wata hadakar siyasa baya idan tana dauke da wadanda suka taba cin gajiyar mulkin da ya tabarbare ba ba.

Asali: Twitter
Ya ce:
“A na magana kan canji, amma irin wadannan mutane sun yi mulki, sun lalata Najeriya, kuma yanzu suna son su sake dawo da wani sabon suna – wannan ba sauyi ba ne, ba kuma adawa ba ce.”
Atiku Abubakar ya ce za su kwace mulki
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa kawancen ‘yan adawa ne kadai zai iya kifar da gwamnatin Bola Tinubu a babban zaben 2027.
A cewar tsohon dan takarar shugaban kasar, akwai bukatar dukkannin jam’iyyun adawa su rungumi dandali daya domin samar da shugabanci na gari da maido da mulkin adalci a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da tawaga ta National Opinion Leaders, ta kai masa inda ya bayyana cewa sabuwar tafiyar siyasa ce wadda za ta bai wa Najeriya sabon salon shugabanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng