Fitaccen Mawaki Ya Ɗauki Abubuwan da ke Faruwa a Najeriya Ya Kai Gaban Shugaban Amurka

Fitaccen Mawaki Ya Ɗauki Abubuwan da ke Faruwa a Najeriya Ya Kai Gaban Shugaban Amurka

  • Fitaccen mawakin Najeriya, Davido ya rubuta wasika ya sika wa Shugaban Amurka Donald Trump kan zaben gwamnan jihar Osun
  • Mawakin ya nuna damuwa kan yiwuwar samun gagarumin tashin hankali da katsalandan a tsarin zaɓen
  • Ya ce al’ummar jihar Osun na da haƙƙin a barsu du yi zaɓe cikin ’yanci, zaman lafiya da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da ƙasashen duniya su sa ido sosai kan zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.

Mawakin ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar tashin hankali, tsoratar da masu zaɓe da kuma katsalandan ga tsarin dimokuraɗiyya yayin da siyasa ke ƙara zafi a jihar gabanin zaɓen.

Davido.
Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido Hoto: @Davido
Source: Instagram

Davido ya yi wannan kira ne a wata wasika da ya tura wa Shugaba Trump, da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 11 ga watan Agusta, 2027. inda ya yi magana kai tsayekan halin da ake ciki a Osun.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya zargi Jingir da rura wutar rikici bayan kalamansa kan Muslim Muslim

Davido ya nemi a kare masu zaɓe

A cikin saƙon, Davido ya ce akwai ƙarin damuwa game da tashe-tashen hankula da ka iya faruwa yayin zaɓen, musamman saboda zafin da siyasar jihar ta shiga.

Ya ce al’ummar Osun na da cikakken haƙƙin yin amfani da ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su na zaɓar shugabanninsu cikin ’yanci ba tare da tsoro ko tsoratarwa ba.

Mawakin ya ce:

“Ba ma son zubar da jini, ba ma son tsoratarwa, muna son zaman lafiya, gaskiya da kuma zaɓe na gaskiya da adalci.”

Davido ya kuma roƙi Shugaba Trump da sauran masu ruwa da tsaki na ƙasa da ƙasa da su sa ido kan yadda za a gudanar da zaɓen domin tabbatar da cewa an kare masu zaɓe tare da mutunta ƙuri’unsu.

Ya nuna damuwa kan tashin hankali

Kiran mawakin na zuwa ne a lokacin da abubuwa ke ƙara zafi a Osun yayin da jam’iyyun siyasa da ’yan takara ke shirin babban zaɓen da zai tantance wanda zai jagoranci jihar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Saura kwana 5 a fara kada kuri'a, an bankado makarkashiyar da ake kullawa

Davido ya kasance yana magana a kai a kai kan abubuwan da suka shafi zaɓen Osun, wanda ya jawo hankalin jama’a saboda fafatawar da ake yi tsakanin gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, da sauran manyan ’yan takara.

Gwamna Adeleke kuma kawun Davido ne, lamarin da ya sa mawakin ke da alaƙa ta musamman da siyasar jihar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana magana da manema labarai a fadar White House Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Getty Images

Abin da Davido yake bukata

Davido ya jaddada cewa babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cewa mazauna Osun sun je rumfunan zaɓe cikin kwanciyar hankali, ba tare da an tsoratar da su ko tilasta musu zaɓen wani ɗan takara ba.

Ya kuma yi kira ga hukumomin da ke da alhakin tsaron zaɓe da gudanar da shi da su tabbatar da cewa an kare masu zaɓe kuma babu wani abu da zai kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya.

Mawakin ya ce sa ido daga ƙasashen duniya na iya taimakawa wajen ƙara tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Osun 2026: an kama kwamishinan Adeleke

An ji cewa rundunar ’yan sandan Osun ta kama Mayowa Adejoorin, kwamishinan muhalli da tsaftar muhalli na jihar kan harbe harben da aka yi a taron APC.

Kamen dai ya janyo martani daga Imole Campaign Council, kungiyar yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke , wadda ta zargi ’yan sanda da nuna son kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262