Mawakin Musulunci Ya Shiga Coci, Ya Rera Wakar Kiristoci da Ta Jawo Magana

Mawakin Musulunci Ya Shiga Coci, Ya Rera Wakar Kiristoci da Ta Jawo Magana

  • Mawaƙin Musulunci, AbdulKabir Alayande, wanda aka fi sani da Ere Asalatu, ya bayyana dalilin da ya sa ya rera waƙar Kirista a cikin coci
  • Ere Asalatu ya ce Yesu Kristi shi ne Annabi Isa da Alƙur’ani ya ambata, yana mai cewa Musulunci bai koyar da ƙin Yesu ba
  • Mawaƙin ya yi kira ga Musulmai su rungumi haƙuri da zaman lafiya, yana mai cewa Musulunci addini ne na haɗin kai, soyayya da salama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Mawaƙin Musulunci, AbdulKabir Alayande, wanda aka fi sani da Ere Asalatu, ya yi martani kan ce-ce-ku-ce da ake yi kansa.

Asalatu ya bayyana dalilin da ya sa ya rera waƙar Kirista a lokacin da ya halarci wani shiri a coci.

Mawakin Musulunci ya kare kansa bayan shiga coci
Mawakin Musulunci a Najeriya, AbdulKadir Alayande. Hoto: Ere Asalatu.
Source: Instagram

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaruma Biola Adebayo a cikin shirinta na tattaunawa, wanda Punch ta bibya, bayan wasu Musulmai sun soki yadda ya yi.

Kara karanta wannan

'Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya': Netanyahu ya yi shagube ga kasar Ingila

Mawakin Musulunci ya jawo ce-ce-ku-ce

Mawaƙin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon da ke nuna shi yana rera waƙar Kirista mai taken “Jesus is the only true friend” a coci ya bazu.

Da yake bayyana dalilinsa, Asalatu ya ce Yesu da ake magana a cikin waƙar shi ne Annabi Isa da Alƙur’ani ya ambata.

Ya ce:

“Wannan Yesu da muke magana a kansa shi ne Annabi Isa a cikin Alƙur’ani, ɗan Maryam, Annabi Muhammad bai musanta Yesu Kristi ba, Ashe ba a aiko shi gare ku ba, Musulunci bai ce mu yi adawa da Yesu ba. Ban san inda suka samo nasu ba.”

Mawaƙin ya kuma gode wa magoya bayansa da masu sukar sa, yana mai cewa kalaman sukar sun taimaka masa wajen gano abubuwan da zai gyara.

Mawakin Musulunci ya sha suka da ya shiga coci
Mawakin Musulunci a Najeriya, AbdulKabir Alayande da aka fi sani da Ere Asalatu. Hoto: Asalatu.
Source: Instagram

Mawakin ya yi nasiha ga wasu Musulmi

Asalatu ya sake tabbatar da cewa zai ci gaba da riƙe addinin Musulunci tare da wa’azinsa har zuwa lokacin tsufa.

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

Ya ce Musulunci addini ne mai tsari, wanda ke koyar da ladabi wajen sanya tufafi tare da bayyana yadda mutum zai gudanar da rayuwarsa.

Sai dai ya soki abin da ya kira tsananin tsauri daga wasu Musulmai, yana mai cewa wasu sun yi tsattsauran ra’ayi wajen fassara koyarwar addini.

Ya tambayi dalilin da ya sa wasu mutane za su tilasta wa wasu yin ibada ko bin wata hanya ta addini, musamman idan ba su taimaka musu wajen samun abin da suke da shi na rayuwa ba.

Asalatu ya ce:

“Ba ku tilasta mini samun nasara a rayuwa ba. Ba ku tilasta mini cin abinci daga tushen kuɗin ku ba. Amma kuna son tilasta mini shiga aljanna. Shin hakan yana da ma’ana? A’a, ba shi da ma’ana.”

Mawaƙin ya yi kira ga mutane da su mutunta bambancin addini, yana cewa kowa ya bauta wa Allah yadda ya fahimta, domin duk abin da mutum ya aikata yana da sakamako, cewar Daily Post.

Ya kuma soki wasu masu cewa daukar hoto zai kai mutum wuta, yana mai nuna cewa bidiyo ma wani nau’i ne na hoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aliyu Ladan ya rasu

Asalatu ya ƙalubalanci wasu masu cewa babu waƙa a Musulunci, yana mai cewa akwai nassoshi da suka yi magana kan ilimi da darussa da ake samu cikin waƙoƙi.

Mawakin Musulunci ya yi murabus daga mukaminsa

Mun ba ku labarin cewa mutane da dama sun sha mamaki bayan murabus din hadimi na musamman ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazak.

Alhaji Alhaji Ibrahim Labeeka wanda mawakin yabo ne ya ajiye aikinsa a yau Laraba 12 ga watan Satumbar 2024.

Labeeka a cikin wata sanarwa ya koka kan yadda yake karbar albashi ba tare da cimma abin da ake bukata ba a ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.