Sauya sheka: PDP ta yiwa Tambuwal barka da dawowa gida
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yiwa gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal barka da zuwa jam’iyyar.
A ranar Laraba, 1 ga watan Agusta gwamnan ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.
Jam’iyyar ta wallafa sakon a shafinta na twitter jim kadan bayan gwamnan ya sanar da sauya shekar tasa.
Ta ce: “Labari da dumi-dumi! Gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal @AWTambuwal ya sauya sheka daga gajiyayar jam’iyyar @APCNigeria zuwa @OfficialPDPNig. Muna masa barka da dawowa gida."
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Talata ya hadu da magoya bayansa a Ilorin, inda anan ya fada masu cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress saboda jajircewarsu akan ya aikata hakan da kuma shige masa gaba da Allah yayi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud
Ya ci gaba da zargin cewa an nuna wariya ga jihar Kwara wajen nade-naden da gwamnatin APC ke yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng