Akwai Matsala: Ana Zargin INEC na Shirin Ayyana Zaben Gwamnan Osun a Matsayin Inconclusive

Akwai Matsala: Ana Zargin INEC na Shirin Ayyana Zaben Gwamnan Osun a Matsayin Inconclusive

  • Kwamitin kamfen Gwamna Ademola Adeleke ta zargi INEC da shirin ayyana zaɓen gwamnan Osun da 'Inconclusive, ma'ana wanda bai kammalu ba
  • Ya ce shirin na da nufin dakile nasarar Adeleke, inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara tsaro a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe
  • Kwamitin yakin neman zaben ya kuma tuna wa INEC umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar kafin ranar wannan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Kwamitin kamfen Gwamna Ademola Adeleke ya zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da shirya ayyana zaɓen gwamnan jihar Osun a matssyin wanda bai kammalu ba.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Bamidele Salam, ya fitar, ya yi kira ga masu sanya ido kan zaɓen da su kasance cikin shiri.

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

Gwamna Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke Hoto: @AAdeleke01
Source: Facebook

Sun zargi INEC da shirin dakile nasara

Kwamitin ya ce ya samu bayanan wani shiri da yake zargi INEC da yi na ayyana zaɓen a matsayin wanda ba a kammala ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Ya kara da cewa hakan na iya zama wani yunkuri na dakile abin da ta kira nasarar Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke.

Ya kuma zargi wasu gwamnoni da shugabannin APC da hannu wajen abin da ta kira yunkurin gaggawa na ƙarshe na kwace nasarar ɗan takararta da kuma yin katsalandan ga ra’ayin masu zaɓe a Osun.

Kwamitin kamfen ya ce:

“Muna son sanar da ’yan Najeriya wani mummunan shiri na Hukumar INEC na ayyana zaɓen gwamnan da aka gudanar a matsayin wanda ba a kammala ba, a wani yunkuri na dakile nasarar da ke gab da zuwa ta Sanata Ademola Adeleke.”

Kwamitin ya nemi kara tura jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun

Kwamitin ya yi kira ga shugaban INEC da ya cika alkawuran da ya sha yi na tabbatar da cewa zaɓen Osun ya kasance cikin ’yanci, adalci da gaskiya, in ji The Nation.

Ya kuma tunatar da INEC, APC da hukumomin tsaro cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tabbatar da cewa ba a yi wa zaɓen katsalandan ba, domin ya zama gwajin yadda za a gudanar da babban zaɓen 2027.

Inec.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya bukaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Darakta-Janar na DSS, Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ƙara tsaro a dukkan cibiyoyin tattara sakamako.

Gwamna Adeleke ya gano shirin APC

A baya, rahoto ya zo cewa gwamnan Osun, Ademola Adeleke , ya zargi jam’iyyar APC da shirin kauce wa tsarin tattara sakamakon zaɓe da aka tanada.

Da yake magana bayan jefa ƙuri’a, Adeleke ya ce ya samu labarin cewa akwai shirin ɗaukar sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe zuwa cibiyar tattara sakamako.

A cewarsa, hakan zai kauce wa tsarin da ya kamata a bi daga rumfunan zaɓe zuwa mazabu sannan zuwa ƙananan hukumomi kafin a kai sakamakon cibiyar tattara sakamakon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262