Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya koma APC a hukumance

Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya koma APC a hukumance

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance
  • Mai Mala Buni, shugaban APC kuma gwamnan Yobe, shine ya mika masa tutar APC a wani gagarumin biki da aka gudanar a Gusau, babban birnin Zamfara
  • Da yake nuna farin cikinsa, Matawalle ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a kan su hada hannu don ciyar da jihar zuwa gaba

Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

A wani taron gangami da aka shirya wa gwamnan na Zamfara a Gusau, babban birnin jihar, a ranar Talata, Mai Mala Buni, gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko na APC ya gabatar da tutar APC ga Matawalle, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya koma APC a hukumance
Gwamna Bello Matawalle ya koma APC a hukumance Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye da hotunan gwamnonin APC da ke Zamfara a yanzu haka don sauyin shekar Matawalle

Matawalle, wanda ya nuna farin cikinsa da yadda aka karbe shi a cikin jam'iyyar, ya yi kira ga hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki don bunkasa jihar.

Ya ce:

“Daga yau, Ni, Bello Matawallen Maradun, gwamnan Zamfara, ina mai farin cikin sanar da ficewata daga PDP zuwa APC. Daga yau, Ni cikakken dan APC ne kuma shugaban APC a Zamfara.
"Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na APC a jihar da su hada kai da ni don gina jam'iyyar da kuma ciyar da jihar gaba."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mahdi kan zargin batanci ga Masari

PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

A gefe guda, mun ji cewa Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta Tsakiya a majalisar dokoki ta kasa, Sanata Hassan Mohammed Nasiha, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Dan majalisar ya sanar da sauya shekarsa a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce ya shawararsa ta ficewa daga PDP ya zama dole saboda rugujewar dimokiradiyyar cikin gida da rabuwar kan PDP a jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel