2027: Ziyarar da Atiku Ya Kai Wa Buhari Ta Sake Tayar da Ƙura a Siyasar Najeriya

2027: Ziyarar da Atiku Ya Kai Wa Buhari Ta Sake Tayar da Ƙura a Siyasar Najeriya

  • Bode George ya soki ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari har gida a jihar Kaduna
  • Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa ya yi zargin cewa ziyarar wata dabara ce da Atiku ya ɓullo da ita domin sake neman takara
  • George ya bayyana cewa PDP ba jam'iyyar mutum ɗaya ba ce kuma alamu sun nuna Atiku ba ya son mutunta tsarin karɓa-karɓa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

George ya soki Atiku ne bisa ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari domin jawo shi cikin haɗakar da ƴan adawa ke shirin yi.

Bode George da Atiku.
Bode George ya caccaki Atiku kan ziyarar da ya kai wa Muhammadu Buhari Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

George ya bayyana rashin jin dadinsa kan wannan mataki na Atiku a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya soki zuwan Atiku wurin Buhari

Ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019 da 2023 ya yi fatali ’ya’yan jam’iyyarsa domin tattaunawa da wani jagora a jam’iyyar APC mai mulki.

Atiku dai ya matsa ƙaimi wajen kira ga hadin gwiwar ’yan adawa domin kafa sabuwar jam’iyya da za ta sauke Shugaba Bola Tinubu daga mulki a 2027.

Sai dai Bode George ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin dabarar Atiku domin muradin kansa, ba don ci gaban PDP ba.

Da yake jawabi a salon tambaya ga Atiku, Bode George ya ce:

"Masu shirin haɗa gagarumar haɗaka menene manufarsu? Ka na jam'iyya mai ƙarfi me yasa ka ke koƙarin fanɗarewa? Ka sa ƙafa ka je wurin Buhari, shi ɗan jam'iyyarmu ne?
"Ka nemi jin ra'ayin ƴan PDP kafin ka tafi wurinsa? PDP ba mallakin mutum ɗaya ba ce, sai kowa ya amince sannan ya kamata a aiwatar, ba zai yiwu ka yi abu don burin kanka kaɗai ba.'

George ya tuna karawar Atiku da Buhari a 2019

Bugu da ƙari, game da ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari, George ya soki matakin yana mai cewa Atiku ya ziyarci mutumin da ya kayar da shi a zabe kamar yaro a 2019.

“Kalli yadda Janar Buhari ke gaisawa da su. Shi mamba ne a PDP? Mun tsayar da kai takara, ya kayar da kai yanzu kai kuma ka sake komawa wurinsa.
"Duba wadanda suka je tare da shi, duk ƴan arewa ne. Ina sauran ’yan jam’iyyarmu? Wannan ya nuna wata manufa ce ta daban," in ji shi.

George ya yi zargin cewa hakan wata dabara ce da Atiku ya ɓullo da ita domin sake samun tikitin takarar shugaban kasa na PDP a karo na uku, ba tare da la’akari da tsarin karba-karba ba.

Ya bayyana damuwa cewa wannan sabon shirin na Atiku na iya haddasa rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu a siyasar Najeriya, rahoton Vanguard.

Wike ya zargi Atiku da karya alƙawari

A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyaja cewa ba zai goyi bayan Atiku Abubakar ba saboda mutum ne mara cika alƙawari.

Wike ya zargi Atiku da wasu manyan kusoshin PDP ciki har da Bukola Saraki da Uche Secondus da saɓawa yarjejeniyar da suka yi a 2019.

Tsohon gwamnan ne jihar Ribas ya ce hakan ya kara tabbatar masa da cewa Atiku ba abin dogara ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262