Tsohon Mataimakin Shugaban PDP Ya Fusata da Shirin Gwamnoni 4 na Komawa APC

Tsohon Mataimakin Shugaban PDP Ya Fusata da Shirin Gwamnoni 4 na Komawa APC

  • Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Bode George ya nuna ɓacinsa ransa kan zargin shirin wasu gwamnoni huɗu na komawa APC
  • George ya bayyana cewa abin kunya ne gwamnoni su bar jam'iyyar da ta yi masu riga da wando har suka samu nasarar hawa kan mulki
  • Ya ce tsarin siyasar Najeriya abin bakin ciki ne domin bai kamata a bar mutum ya bar jam'iyyar da ta ɗauki ɗawainiyarsa har ya ci zaɓe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban jigo a jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya bayyana matukar bakin ciki kan rahotannin cewa wasu gwamnoni na shirin ficewa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

George, tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa ya kira hakan da cin amanar jam’iyyar da ta ba su damar ɗare wa kan madafun iko.

Bode George.
Bode George ya caccaki gwamnonin PDP da ke shirin ficewa zuwa APC Hoto: Chief Bode George
Asali: Facebook

Bode George ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi shi a gidan talabijin na Arise TV ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

George ya soki shirin sauya shekar gwamnonin PDP

Ya ƙara da cewa abin kunya ne gwamnonin su yi watsi da jam'iyyar da ta tallafa masu har suka samu mulki.

George ya ce:

"Tsarin da muke tafiya da shi yanzu abin takaici ne. Ta ya jam'iyyar da ta baka dama ka wakilci jama'a amma tun kafin ka gama wa'adinka ka fara ƙoƙarin barinta?
"Waɗannan gwamnonin sun ba ni kunya, ban ji daɗin abin da suke yunkurin yi ba."

Jigon PDP ya bada misali da tsarin Afirka ta Kudu

George ya tuna da lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa Afirka ta Kudu a zamanin tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua domin warware rikicin siyasa a can.

Ya bayyana yadda tsarin siyasa na Afirka ta Kudu ya bambanta, inda jam’iyya ce ke tsayawa takara, ba mutum ba, kuma ana mutunta tsarin jam’iyya sosai.

“Shi ya sa a can, idan aka ce jam’iyya na saman kowa, to babu wanda zai musanta," in ji shi.

Bode George ya caccaki gwamnonin da suka nemi takara bisa tsari da manufofin PDP, amma yanzu suna kokarin barin jam’iyyar zuwa wata daban.

“Jama’a sun zabe su ne saboda tsare-tsaren PDP. Yanzu kuma suna kokarin komawa APC? Wane ci gaba APC ta kawo na daban?”

Waɗanne gwamnoni ne ke shirin komawa APC

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke nuna cewa gwamnoni hudu na PDP na shirin sauya sheka zuwa APC domin tallafawa Shugaba Bola Tinubu ya yi tazarce a 2027.

Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya ayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu a bainar jama'a.

Gwamnonin PDP.
George ya ce cin amana ne gwamnonin PDP su koma APC Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Sai kuma Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta, Peter Mbah na Enugu, da Gwamna Sim Fubara na Ribas (wanda aka dakatar) waɗanke ke nazari kan lamarin.

George ya bayyana hakan a matsayin abin kunya ga gwamnonin, yana mai cewa za su jira su ga abin da zai faru, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Jigon PDP ya soki zuwan Atiku wurin Buhari

A wani labarin, kun ji cewa jigon PDP, Bode George ya caccaki ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kwanan nan.

George ya bayyana cewa wannan mataki da Atiku ya ɗauka ba don ci gaban PDP ba ne, sai dai don cika muradin kansa.

Ya nuna damuwarsa kan cewa wannan sabon shirin na Atiku na iya haddasa rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu a siyasar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262