Atiku Ya Sake Gamuwa da Matsala a Yunkurinsa na Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa zai yaƙi Atiku Abubakar idan ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa
- Fayose wanda ya yi mulki a PDP ya ce ba zai yiwu ɗan Arewa ya gama shekaru takwas kuma wani ɗan Arewa ya karbi mulkin Najeriya ba
- A cewarsa, idan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar zarcewa, da kansa zai fito da yaƙi duk ɗan Kudun da ya nemi mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana cewa ba zai mara wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, baya ba idan ya sake takara a 2027.
Ayo Fayose ya ce zai kuma yaƙar Atiku kamar yadda ya yi a zaɓen 2023 matukar aka sake tsayar da shi takara.

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na Channels TV ranar Juma’a, 18 ga watan Afrilu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na fito fili na yaƙi Atiku a 2023, kuma zan sake fada karo na biyu, idan Atiku ya sake fitowa takara, zan sake yaƙarsa. Ya kamata ya ɗauki darasi."
Fayose ya faɗi tushen rikicin PDP
A cewar Fayose, rikicin jam’iyyar PDP ya fara ne tun lokacin da aka yanke shawarar mayar da mulki zuwa Arewa bayan shekaru takwas na Muhammadu Buhari.
"Yayin da dan Arewa ya kammala shekara takwas a kan mulki, kamata ya yi mulki ya koma Kudu, ko daga Gabas, Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu."
"Waɗanda suka amince mulki ya kara komwa yankin Arewa ne suka janyo wannan rikicin."
"Ba sai ka so Nyesom Wike ba, ko Peter Obi ba, amma ya kamata a samu wata yarjejeniya da kowa zai riƙa girmamawa wacce za ta tanadi tsarin karɓa-karɓa tsakanin Kudu da Arewa."
- In ji Fayose.

Asali: Facebook
Fayose ya yaƙi Atiku a zaɓen 2023?
A 2024 ne Fayose ya fito bainar jama'a ya sanar da cewa ya yaƙi Atiku Abubakar a zaɓen 2023, yana mai cewa ya yi haƙa ne don ci gaban ƙasar nan.
"Ka da ku ɗauka da wata manufa amma dai yakar Atiku na yi ɗari bisa ɗari, Najeriya ta fi ƙarfin PDP ko APC," in ji shi.
Ya jaddada cewa domin PDP ta samu daidaito da tsarin shugabanci, dole ne ta nuna adalci da gaskiya, kuma ta guji keta yarjejeniyoyi da suka shafi tsarin mulki.
Fayose ya kuma ce bayan kammala mulkin Bola Ahmed Tinubu idan Allah Ya ba shi damar wa’adi na biyu, dole ne mulki ya koma Arewacin ƙasar.
Atiku ya sha alwashin kafa mulkin adalci
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce haɗakar ƴan adawa za ta dawo da mulkin adalci a Najeriya.
Atiku ya ce za su rungumi kowace jam'iyya matukar za ta taimaka wajen tabbatar da manufarsu ta samar da kyakkyawan shugabanci ga ƴan ƙasa.
Wazirin Adamawa ya yi kira ga matasa tare ba su shawara da kada su sayar da makomarsu saboda wasu ‘yan kudi da za a basu, wanda ba su taka kara sun karya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng