'An Gaji da Addu'a yanzu': Malami Ya Fadawa Tinubu Gaskiya, Ya Nemo Masa Mafita
- Fasto Tunde Bakare ya bukaci Shugaba Tinubu ya daina “yin kamar na Allah ne shi" kuma ya rungumi tawali’u da karɓar shawara domin ceto Najeriya
- Bakare ya bayyana cewa addu’o’i sun isa haka, yanzu lokaci ne na ɗaukar matakai domin kaucewa mafiyar siyasa da rugujewar dimokuraɗiyya
- Faston ya bukaci a duba lafiyar kwakwalwar ‘yan siyasa kafin takara, tare da kafa sabuwar cibiyar raya tattalin arziki mai da sauran bangarori
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Fasto Tunde Bakare da ke kula da Cocin 'Citadel Global Community' ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu da lalacewar tattalin arziki.
Bakare ya shawarci Shugaba Tinubu da ya daina “wasa da Allah” kuma ya rungumi tawali’u da karbar shawarwari domin ceto Najeriya.

Asali: Facebook
Fasto ya shawarci Tinubu ya nemo mafita ga kasa
Yayin jawabin halin ƙasa a cocinsa dake Lagos, ya ce lokaci ya yi da shugaban ya aiwatar da tsari mai kyau don ceto Najeriya, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ’yan Najeriya sun yi addu’a na tsawon lokaci, yana mai cewa kira na ƙara addu’a yanzu ya zama kamar al'adar addini wanda kowa ya gaji da hakan yanzu.
Bakare ya gargadi shugabanni da su ɗauki mataki da gaggawa domin hana ƙasar faɗuwa hannun kungiyoyin mafiyar siyasa da tabarbarewar doka.
Ya ce:
“Masu imani sun gaji da addu’a, kuma kiran yin addu’a yanzu ya zama kamar al’adar addini kawai.
“Wasu sun yanke shawarar cewa addu’a ta isa haka, sai dai idan ba a ɗauki matakai ba, rashin inganta talakawa zai haddasa tabarbarewa sosai.”
“Ta hanyar fuskantar gaskiya da jarumtaka za mu iya farfado da ƙasa da kuma ruhohinmu da suka karye."

Asali: Facebook
Fasto ya ce an gaji da addu'a a Najeriya
Ya tunatar da yadda ya yi addu’a da ba da shawara ga gwamnatin Tinubu a ranar Lahadi, 12 ga Janairu, 2025 don gujewa rugujewar doka.
Bakare ya ce bayan waccan addu’a, shugabannin ƙasar sun kasa nuna halin kirki da tawali’u da ake buƙata a irin wannan lokaci, Premium Times ta ruwaito.
Ya ce abin da ake gani tun farkon shekarar 2025 shi ne danniya da amfani da iko fiye da kima ta hanyar tauye dokar ƙasa.
Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi tunani a kan wannan magana: “Babu wanda ya isa ya amince da shi da iko mara iyaka.”
An fadi lokacin da Tinubu zai dawo
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan sukar da ake yi game da rashin dawowar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gida Najeriya.
Idan ba a manta ba, tun a ranar 2 ga Afrilun shekarar 2025, Tinubu ya bar Najeriya zuwa Faransa domin wata ziyarar aiki ta mako biyu.
Yayin da fadar shugaban kasa ke fadin lokacin da Tinubu zai dawo gida, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu na tafiyar da mulki daga kasar waje.
Asali: Legit.ng