"Ba Ya Cika Alƙawari," Wike Ya Tuna Abin da Atiku Abubakar Ya Masa a 2019
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai marawa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar baya ba
- Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce Atiku mutum ne mara cika alkawari domin ya taɓa aba yarjejeniyar da suka yi a 2019
- Ya ce babu waani dalili da zai sa ya goyi bayan Atiku saboda ya san halinsa, yana mai bayyana cewa ba abin dogaro ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar, mutum ne mara cika alkawari.
Wike ya zargi Atiku da wasu manyan kusoshin PDP ciki har da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da saɓawa yarjejeniyar da suka yi a 2019.

Asali: Facebook
Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, kamar yadda The Cable ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya jaddada cewa goyon bayan Bola Tinubu da ya yi a zaben 2023 shi ne abin da ya dace.
Wike ya faɗi abin da ya sa ya guji Atiku
Wike ya ce duk da jam’iyyar APC tana cikin wani hali saboda gazawar gwamnatin Buhari, bai ga Atiku a matsayin mafita ba, don haka ya zabi goyon bayan wanda yake ganin zai kawo sauyi a Najeriya.
Ministan Abuja ya ce:
"Na kafe a kan matakin da na ɗauka cewa ba zan mara wa dan takarar PDP baya ba. A wancan lokaci, APC ta na tsaka mai wuya saboda matsalolin gwamnatin Buhari.
"A lokacin na tsaya na yi nazari kan wanda ya kamata na marawa baya, amma idan ka duba Atiku, za ka gane ba shi ne mafita ba, shi ya sa na kauce masa.”
Wane alkawari Atiku ya saɓa wa Wike?
Mista Wike ya bayyana cewa Atiku ya ci amanar yarjejeniya da suka kulla a 2019 tare da Bukola Saraki da tsohon shugaban PDP na ƙasa, Uche Secondus.
“Atiku ba ya cika alkawari, wannan na fada ne bisa tabbaci. A 2019, Atiku, Saraki da Secondus sun zo wurina suka ce ni zan ba da Antoni-Janar da kuma Ministan Man Fetur.
"Amma bayan mun sha kaye a zaɓen, mutumin da za a nada AG ma bai san lokacin da aka kafa tawagar lauyoyi ba kafin shiga kotu.”
- Nyesom Wike.
Tsohon gwamnan ya ce hakan ya kara tabbatar masa da cewa Atiku ba abin dogara bane.
“Na san tun farko Atiku ba zai cika alkawari ba, kuma ban taba sa rai daga gare shi ba. Don haka yanzu zan ce zan goyi bayansa? Ai hakan ba zai yiwu ba," in ji shi.
Wike ne matsalar PDP
Muhammad Usman ya shaida wa Legit Hausa cewa duk wani mai ruwa da tsaki a PDP tun daga matakin ƙasa har zuwa mazaɓu ya san waye matsalar jam'iyar.
Matashin ɗan siyasar wanda jigon PDP ne a karamar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina ya ce PDP ba zata taɓa shawo kan rikinta ba matukar aka bar bara gurbi irinsu Wike.
Ya ce:
"Ba zai yiwu a ce mutum yana cikin jam'iyya kuka yana yaƙarta ba, babu dokoki kenan, koma me Atiku ya masa bai kamata ya ci amanar PDP ba.
"Ba za a taɓa warware rikicin PDP ba matukar ba kori mutane irinsu Wike ba, kowa ya san gaskiya, kawai dai wasu shugabanni na amfana da shi ne shi yasa yake cin karensa babu babbaka.
2027: Wike ya caccaki jam'iyyarsa ta PDP
A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce ga dukkan alamu babbar jam'iyyar hamayya watau PDP ba ta shirya tunkarar zaɓen 2027 ba.
Wike ya ce PDP ba ta da tsarin da za ta iya ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki, ya kuma soki yadda jam'iyyar ke tafiyar da harkokinta na cikin gida.
Kalaman tsohon gwamnan na zuwa ke kwanaki ƙalilan gwamnonin PDP sun nesanta kansu daga shirin haɗakar ƴan adawa karkashin Atiku Abubakar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng