Atiku Abubakar Ya Fadi Darasin 2027 da Ya Dauka daga Wasan Arsenal da Madrid

Atiku Abubakar Ya Fadi Darasin 2027 da Ya Dauka daga Wasan Arsenal da Madrid

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa nasarar da Arsenal ta samu a gasar Zakarun Turai ta karfafa masa gwiwa
  • Atiku na ganin wasan da ya ba Arsenal damar kai wa matakin kusa da na karshe a gasar, ya nuna muhimmancin dunkulewa da hada karfi waje guda
  • Atiku Abubakar ya kara da cewa hakan ya kara masa kwarin gwiwa kan hadakar jam’iyyun da suka kuduri aniyar kwato mulki daga jam’iyyar APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwarsa a siyasar Najeriya, musamman dangane hadakar jam'iyyu.

Wannan kwarin gwiwar, ya samo asali ne daga nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu a kan Real Madrid a gasar zakarun Turai.

Atiku
Atiku ya ce nasarar Arsenal ta kara masa kwarin gwiwa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya jaddada cewa za a iya cimma nasara matukar an dunkule waje guda, an hada karfi da karfe domin cimma manufa daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar da Arsenal ta samu ya ba ta damar kaiwa zagaye na daf da karshe karo na farko tun bayan shekarar 2009.

Nasarar Arsenal ta yi wa Atiku dadi

BBC Hausa ta ruwaito cewa Real Madrid ta sha kashi a hannun Arsenal da ci 2-1 a wasan na biyu na kusa da na kusa da na karshe a gasar zakarun Turai.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Bukayo Saka a zagaye na biyu, duk da cewa ya kasa cin fenariti a zagaye na farko.

A daf da za a tashi daga wasan ne Gabriel Martinelli ya kara ta biyu, wanda hakan ya tabbatar da cewa Gunners sun doke Real Madrid a gida da waje a bana.

Atiku
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Da yake bayyana ra'ayinsa kan wasan, Atiku ya ce:

“Arsenal ta koya mana darasi a kan yadda ake hade karfi a cikin hadaka. Nasara tabbas za ta tabbata idan muka tsaya tsayin daka tare da dunkulewa wuri guda.”

Martanin jama’a ga Atiku kan wasan Arsenal

’Yan Najeriya da ke bibiyar Atiku Abubakar a Facebook sun mayar da martani kan sakon nasa, inda da dama suka bayyana goyon bayansu ga kalamansa, amma sun nesanta kansu da hadakarsa.

Idara Umoh ya rubuta:

Erhunmwunse Agbama Napoleon ya wallafa : A 2027 ba, ko 2031. Ko a zuriyar da ke zuwa nan gaba. Kai ne daya daga cikin dalilan da ya sa Najeriya ke cikin halin da take ciki yanzu. Ka yi amfani da hadaka wajen kifar da GEJ, yanzu kana tunanin hadaka za ta kai ka ga nasara? Ka farka, ranka ya dade. Ka je ka nemi gafara daga GEJ."

Sadiq Suleiman ya ce:

“Idan fa don Arsenal ne, ba za mu shiga wannan hadakar ba.”

Sani Musa ya ce:

"Insha Allah PSG za ta fitar da Arsenal.”

Manu Fagge ya rubuta cewa:

“Mu ’yan Real Madrid ba za mu zabe ka ba.”

Ibrahim Halliru kuwa ya ce:

“Haka zaka lashe shugaban kasa a 2027 in sha Allah.”

Atiku na son a shiga kawancen jam'iyyunsa

A baya, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa hadakar jam’iyyun adawa ita ce hanyar da za ta kai Najeriya ga cigaba da shugabanci nagari a zaben 2027 mai zuwa.

A cewar Atiku, jam’iyyun adawa za su rungumi kowane dandali da zai taimaka musu wajen cimma wannan buri na kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kuma dawo da adalci.

Wannan bayani na Atiku na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan da Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP ta nesanta kanta da kawancen jam’iyyun adawa da Atiku ke kokarin jagoranta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.