NNPP Ta Fusata, Ta Yi Martani a kan Zargin Ganduje na cewa Suna Fama da Rabuwar Kai
- Sakatarenbyada labaran APC, Ladipo Johnson ya bayyana cewa maganganun shugaban APC, Abdullahi Ganduje, kan NNPP ba su da amfani
- Ya ce Ganduje bai fahimci ma’anar kalmar rabuwar kai ba, inda ya shawarce shi da ya duba ƙamus kafin yin irin waɗannan kalamai
- Johnson ya kara da cewa akwai waɗanda aka kora daga NNPP da ke amfani da hukuncin kotu na bogi suna yaudarar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sakataren yada labarai na ƙasa na jam’iyyar New NNPP, Ladipo Johnson, ya yi martani a kan kalaman shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Ya bayyana cewa kalaman shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, game da NNPP ba su da wani tasiri ko amfani.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Johnson ya karyata ikirarin Ganduje da ke cewa NNPP na fama da rikici da rabuwar kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa tun da farko ma, suna daukar maganganun Ganduje a matsayin marasa amfani da wani tasiri a yadda suke gudanar da tafiyarsu.
Jam'iyyar NNPP ta caccaki Abdullahi Ganduje
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Johnson ya ƙara da cewa Abdullahi Ganduje bai fahimci ma’anar kalmar "rarrabuwar kai" ba.
Ya kuma kara da ba shi shawarar cewa ya kamata ya duba ƙamus domin fahimtar kalmomin kamar rabuwar kai.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Ganduje na bukatar ya bude ƙamus ya duba ma’anar kalmar 'rabuwar kai'. Ba mu da wata rarrabuwar kai a cikin NNPP. Ba mu da wani ɓangare na daban ko ƙungiya ta daban."
Jam'iyyar NNPP ta soki tsofaffin 'ya'yanta
Johnson ya bayyana cewa mutanen da Ganduje ke nufi sun riga sun fice daga jam’iyyar, kuma suna amfani da tsohuwar tambarin jam’iyya da an daina amfani da shi.
Ya ce:
"Wasu ne da aka kori daga jam’iyya, amma suna ta amfani da tsohon tambari da aka sauya tuni. Wannan tambarin ba ya gaban INEC. INEC ta san waye shugaban NNPP na ƙasa."
A cewar Johnson, waɗanda aka kora daga NNPP sun je wani lungu na jihar Abia inda suka samu hukuncin kotu ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya ce:
"Ka ga, waɗannan mutane masu tayar da zaune tsaye sun je wani lungu a jihar Abia, suka samo hukuncin kotu na gaggawa."
"Suka kai kansu gaban kotu, suka gabatar da tsohuwar kundin tsarin mulki. INEC ba ta halarta ba. Mu ma ba mu halarci zaman kotun ba."
Johnson ya ci gaba da zargin cewa waɗanda aka kore sun yaudari kotun da aka samu wannan hukuncin.
Ganduje ya yi martani ga jigon NNPP
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani mai zafi kan kalaman jigon jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima.
A cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa Ganduje kan harkar wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar, ya bayyana cewa Buba Galadima sananne ne da rashin aminci a siyasa.
Hakan na zuwa ne yayin da rikici ke kara kamari tsakanin APC da NNPP, musamman dangane da matsayin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na kokarin koma wa jam'iyya mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng