'Ka Nemi Yafiyar Tinubu, Shettima': Sabon Sharaɗin da APC Ta Gindaya ga Kwankwaso

'Ka Nemi Yafiyar Tinubu, Shettima': Sabon Sharaɗin da APC Ta Gindaya ga Kwankwaso

  • Jam’iyyar APC ta Kano ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi gafara daga Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin ya shiga APC
  • Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya ce suna maraba da Kwankwaso da sauran masu sauya sheka, amma sai sun bi wasu sharudda
  • Abbas ya ce APC ba za ta karɓi duk wanda ya zagi shugabanninta ba tare da ya ba da hakuri a fili ba, ta haka ne za a iya yin tafiya tare da juna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jita-jitar cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC a yan kwanakin nan sai kara karfi take yi.

Jam'iyyar APC a jihar Kano ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso da duk wanda ke son shiga jam’iyyar su nemi gafara daga shugabanni.

APC ta fadi sharadi ga Kwankwaso kafin dawowa cikinta
APC a Kano ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi gafarar Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Twitter

Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce suna maraba da duk masu son sauya sheka, amma sai sun cika sharuddan da aka gindaya, rahoton The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta magantu kan jita-jitar zuwan Kwankwaso APC

A baya, mun ruwaito cewa NNPP ta karyata ikirarin APC na cewa Rabiu Kwankwaso yana shirin komawa jam’iyyar da kuma cewa NNPP ta mutu.

Mai magana da yawun NNPP ya ce Abdullahi Ganduje na fargaba ne saboda tasirin Kwankwaso da ganin cewa ya fi shi daraja a siyasa.

Shugabannin NNPP a matakin jihohi sun caccaki Ganduje suna cewa babu wani shiri da 'yan jam'iyyarta suka yi na komawa APC a Najeriya.

APC ta na jin zafi kan cin mutuncin Bola Tinubu

Abbas ya ce akwai yan siyasa da yawa da suka ci mutuncin Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

'Dan siyasar bai kama sunan kowa ba, amma da alama da Kwankwaso yake.

A cewarsa:

“Muna kira da babbar murya ga duk wadanda suka taba zagin Shugaba Tinubu da Shettima su nemi afuwa a fili domin girmamawa.”
APC ta buƙaci Kwankwaso ya kaskantar ta kansa kafin ta karɓe shi
Jam'iyyar APC a Kano ta bukaci Rabiu Kwankwaso ya roki Tinubu da Shettima yafiya kafin sauya sheka zuwa cikinta. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

APC na maraba da masu son dawowa

Abbas ya ce APC na cigaba da karɓar masu sauya sheka daga sauran jam’iyyu, musamman ganin ana rade-radin Kwankwaso zai sauya sheka zuwa APC.

A cewarsa, jam'iyyar APC ce kadai mafita ga Kwankwaso saboda ya lalata dangantakarsa da sauran gidajen siyasa da ke cikin kasar nan.

Abbas ya ce:

“Ba tare da nuna bambanci ba, muna maraba da sababbin 'yan jam’iyya domin su yi rajista a mazabunsu kamar yadda kundinmu ya tanada.
“Duk wani sabon ko tsohon mamba zai iya tsayawa takara ko kada kuri'a, babu wani fifiko na musamman.”

Shugaban ya ce wasu 'yan siyasa sun zama tamkar kututture a siyasa, don haka suna kokarin neman mafaka a APC don dawo da martabarsu.

Buba ya ƙaryata labarin komawar Kwankwaso APC

A wani labarin, dattijo kuma jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya ce babu wani shirin Rabi'u Musa Kwankwaso na sake komawa APC mai mulki.

Buba Galadima ya zargi shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje da mutanensa da yawan jawo maganar Kwankwaso a kafafen sadarwa domin bukatar kansa.

Injiniya ya kara da cewa 'yan siyasa marasa manufa, da suka gaza ne ke maganar sabon zabe a tsakiyar wa'adin gwamnatinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.