'Yan APC Sun Ja Layi, Sun Yi Watsi da Batun Komawar Kwankwaso Jam'iyyar

'Yan APC Sun Ja Layi, Sun Yi Watsi da Batun Komawar Kwankwaso Jam'iyyar

  • Ƙungiyar masu buƙata ta musamman na jam'iyyar APc reshen jihar Kano sun bayyana matsayarsu kan komawar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar
  • Sun bayyana cewa ko kaɗan ba da maraba da tsohon gwamnan na jihar Kano zuwa cikin APC saboda yadda yake tafiyar da harkokinsa
  • Sun yi zargin cewa idan ya shigo APC, zai yi ƙoƙarin maida ita mallakinsa kamar yadda ya yi wa waɗanda ya taɓa shiga a baya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƙungiyar masu buƙata ta musamman na APC a jihar Kano, sun bayyana matsayarsu kan batun komawar Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar.

Ƙungiyar ta nuna ƙin amincewarta da raɗe-raɗin cewa ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa APC.

Rabiu Musa Kwankwaso
'Yan APC ba su son Kwankwaso ya shigo jam'iyyar Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta, Kwamared Aminu Muazu Fagge, a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan APC ba su maraba da Kwankwaso

Ƙungiyar ta ce ta ƙi amincewa da komawar Kwankwaso jam’iyyar APC ne saboda salonsa na yin kaka-gida a jam'iyyu, da yiwuwar maida APC kamfaninsa na ƙashin kansa kamar yadda ya yi a jam'iyyunsa na baya.

Ƙungiyar ta ce duk da cewa tana maraba da kowane mutum da zai shigo domin bayar da gudunmawa ta gaskiya wajen bunƙasa jam’iyyar, ba za ta lamunci wani da zai ɗauki jam’iyyar a matsayin mallakarsa ba.

"Ƙungiyar masu buƙata ta musamman na APC reshen jihar Kano, wacce ke wakiltar muradun mambobinta, tana bayyana cikakken ƙin amincewarta da yiwuwar dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar APC.”
“Wannan matsaya ta fito ne daga jajircewarmu na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bunƙasa haɗin kai a jam’iyya."
"Manufar Kwankwaso ta ƙashin kansa za ta lalata zaman lafiya da ci gaban jam’iyya, zai maida APC kamar kamfaninsa, kamar yadda ya yi a wasu jam’iyyun da ya yi a baya."

Rabiu Musa Kwankwaso
'Yan APC ba su maraba da shigowar Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook
“Muna jaddada biyayyarmu mara yankewa ga shugabancin jam’iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Hon. Abdullahi Abbas Sanusi. Jagorancinsu ya yi daidai da ɗabi’u da ƙa’idojin jam’iyyar.”
"Muna maraba da duk wanda ke da niyyar bayar da gudunmawa ta gaskiya wajen ci gaban jam’iyyar APC, tare da nuna rashin yarda da duk wani da zai kawo rarrabuwar kai, domin APC ba mallakin mutum daya ba ce, jam’iyya ce ta kowa da kowa a Najeriya."
"Mun ɗauki ƙawance, zaman lafiya da ci gaban jam’iyya a matsayin muhimman ginshiƙai.”

- Kwamared Aminu Mu'azu Fagge

NNPP ta magantu kan komawar Kwankwaso APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta yi magana kan raɗe-raɗin cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC.

Jam'iyyar NNPP ta musanta batun, inda ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan bai da shirin komawa jam'iyya mai mulki.

NNPP ta kuma ƙaryata kalaman da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kan cewa Kwankwaso zai koma jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng