Barau Ya Ragargaji NNPP, Ya ce Manyan Mutanen Kwankwaso za Su Koma APC
- Wasu fitattun 'yan Kwankwasiyya da ɗan takarar shugaban ƙaramar hukuma a Tudun Wada sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC
- 'Yan siyasar sun yi watsi da jar hularsu tare da bayyana goyon bayansu ga APC saboda manufofinta na ci gaban jama’a
- Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa NNPP ta ragu sosai a jihar Kano yayin da jiga-jigan jam’iyyar ke ta sauya sheƙa zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wasu fitattun 'yan jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ranar Juma’a.
Mambobin Kwankwasiyya Scholars da ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Tudun Wada a ƙarƙashin NNPP, Hon. Faruq Abdulrazak Musa sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar NNPP.

Asali: Facebook
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasar sun sauya shekar ne yayin wata ziyarar da suka kai gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a Abuja.
Hon. Faruq da magoya bayansa sun bayyana cewa suna goyon bayan jam’iyyar APC saboda manufofinta da ayyukan ci gaban al’umma da suka fara gani a kasa.
Kano: Matasan NNPP sun rungumi APC
Mambobin Kwankwasiyya Scholars, ƙarƙashin jagorancin Hon. Ahmad Yusuf Maidoki, sun bayyana cewa sun gaji da rashin tabbas a tafiyar Kwankwasiyya.
A yayin ziyarar da suka kai wa Sanata Barau, sun yi watsi da jan hularsu – alamar tafiyar Kwankwasiyya – tare da rungumar jam’iyyar APC.
An bayyana cewa sauya sheƙarsu wani yunkuri ne na kara karfafa APC a Najeriya da kuma kawo cigaban al’umma.
Barau Jibrin ya ce NNPP ta ragu a Kano
A cewar Sanata Barau Jibrin, guguwar sauya sheƙa da ke ci gaba da girgiza jam’iyyar NNPP ta samo asali ne daga ayyuka da dokoki masu amfani da APC ke aiwatarwa ga al’umma.
Ya ce a halin yanzu NNPP na da ƙarancin tasiri a wasu sassan yankin Kano ta Tsakiya, kuma babu wani ƙarfi da take da ita a Kano ta Arewa da Kano ta Kudu.
Sanata Barau ya kuma bayyana cewa fitattun jiga-jigan jam’iyyar daga waɗannan yankuna suna dab da komawa APC.

Asali: Twitter
APC ta yi maraba da sababbin mambobi
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa APC za ta ba sabbin mambobin kulawa da adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.
A yanzu haka dai ana saka ido domin ganin manyan 'yan NNPP da Kwankwsiyya da Sanata Barau ya ce suna shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Tsofaffin yan majalisa sun ba Barau matsayi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar tsofaffin 'yan majalisar Kano sun zabi Sanata Barau Jibrin sun ba shi matsayin uban kungiya.
Shugabannin tsofaffin 'yan majalisar sun bayyana cewa an zabi Sanata Barau ne lura da yadda yake kawo cigaba a Kano da Najeriya.
A na shi bangaren, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa zai cigaba da kokari wajen kawo cigaba mai dorewa a fadin kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng