Ganduje: NNPP Ta Yi Bayani kan Rade Radin Komawar Kwankwaso APC
- Jam’iyyar NNPP ta karyata ikirarin APC na cewa Rabiu Kwankwaso yana shirin komawa jam’iyyar da kuma cewa NNPP ta mutu
- Mai magana da yawun NNPP ya ce Abdullahi Ganduje na fargaba ne saboda tasirin Kwankwaso da ganin cewa ya fi shi daraja a siyasa
- Shugabannin NNPP a matakin jihohi sun caccaki Ganduje suna cewa babu wani shiri da 'yan jam'iyyarta suka yi na komawa APC a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ce-ce-ku-ce ya dabaibaye harkokin siyasa tsakanin jam’iyyun APC da NNPP bayan furucin da shugaban APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi na cewa NNPP ta mutu.
Bayan cewa NNPP ta mutu, Abdullahi Ganduje ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso yana shirin dawowa jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa NNPP ta fito karara ta karyata zargin, ta bayyana cewa Kwankwaso ba shi da niyyar dawowa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, jam'iyyar ta ce Kwankwaso na kan kokarin farfado da NNPP tare da tuntubar ‘yan Najeriya don fuskantar 2027.
Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya ce furucin Ganduje ba shi da wani tasiri, yana mai cewa shugaban APC na cikin firgici da tsoron tasirin siyasar Kwankwaso.
Kwankwaso: NNPP ta musanya maganar Ganduje
A ranar Talata, Ganduje ya bayyana cewa NNPP ta riga ta mutu yayin da yake karbar wasu magoya bayan Tinubu a sakatariyar APC ta kasa da ke Abuja.
Ya kara da cewa an kera akwatin jana’izar NNPP saura a hako kabari, kuma APC za ta karbi Kwankwaso idan ya dawo gida.
Sai dai NNPP ta ci gaba da kalubalantar furucin, inda shugabanta na jihar Osun, Dr Tosin Odeyemi, ya ce APC ba ta da damar sukar kowa, ganin irin matsalolin tattali da ta jefa ‘yan kasa a ciki.
VON ta wallafa cewa shugaban NNPP a Kano, Hashimu Dungurawa ya kara tabbatar da cewa Kwankwaso ba zai koma APC ba.
NNPP ta ce APC na son jawo Kwankwaso
Dr Odeyemi ya zargi APC da kokarin jan Sanata Kwankwaso ne kawai domin su amfana da shahararsa a Najeriya.
Ya ce Kwankwaso mutum ne mai hangen nesa, kuma ba zai hada kai da jam’iyyar da ta cutar da Najeriya ba.
Dr Tosin Odeyemi ya kara da cewa:
“Ya fi dacewa Ganduje ya maida hankali wajen gyaran jam’iyyarsu da ta gaza fiye da ya tsaya kan karya da kokarin shafa kashin kaji wa Kwankwaso.”

Asali: Twitter
Ganduje ya ce Abuja za ta dawo karkashin APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce bai kamata a ce birnin tarayya Abuja na karkashin 'yan adawa ba.
Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne yayin karbar masu sauya sheka daga jam'iyyun adawa zuwa APC a wani gagarumin taro a Abuja.
Shugaban jam'iyyar ya ce za su yi abin da ya dace wajen ganin shugaba Bola Tinubu da APC sun samu nasara a Abuja a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng