Buba Galadima Ya Yi Watsi da Rade Radin Kwankwaso zai Koma APC

Buba Galadima Ya Yi Watsi da Rade Radin Kwankwaso zai Koma APC

  • Jigon NNPP, Buba Galadima, ya ce babu wani shiri na Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai sake komawa jam’iyyar APC mai mulki
  • Ya zargi Abdullahi Umar Ganduje da mutanensa da yawan jawo maganar Kwankwaso a kafafen yada labarai domin bukatar kansa
  • Injiniya Buba, ya kara da cewa 'yan siyasa marasa manufa, da suka gaza ne ke maganar sabon zabe a tsakiyar wa'adin gwamnatinsu
  • Dattijon ya ba da tabbacin cewa babu wanda zai so komawa APC saboda Ganduje, sai don ikon da Tinubu ke da shi a jam’iyya mai-cin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jigo a NNPP, Buba Galadima, ya musanta rahotannin da ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa APC.

A cewar Buba Galadima, jam’iyyar NNPP na ci gaba da nuna wa ’yan Najeriya irin nagartar da take da ita, tare da alkawarin gudanar da mulki bisa gaskiya da rikon amana.

Kwankwasi
Buba Galadima ya musanta cewa Kwankwaso zai koma APC Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje/Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Buba Galadima ya ce, masu yawan magana kan zabe a tsakiyar wa’adin mulki ba su da wani abin yi a siyasa sai surutan kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya-bayan nan ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hasashen cewa Sanata Kwankwaso zai dawo APC.

‘Kwankwaso ba zai koma APC ba,’ Buba

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abdullahi Ganduje ya ce jam’iyyar APC na jiran dawowar Kwankwaso ciinta, kuma ana yi masa maraba.

Amma a martaninsa, Buba Galadima ya ce ba wani mutum mai mutunci da hankali a Kano ko wani bangare na kasar nan da zai yi alfahari da APC a karkashin shugabancin Ganduje.

Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya kara da cewa Ganduje na amfani da jam’iyyar NNPP ne domin jawo hankalin kafafen yada labarai, kuma da ba don ikon Bola Tinubu ba, da ba zai taba zama shugaban jam’iyya ba.

Ya bayyana cewa:

“Ni daga gare ku na fara jin wannan batu. To idan muka koma APC, shin mutane za su ji daga bakin Ganduje? Tinubu ne kadai zai iya sa Ganduje ya zama shugaban jam’iyya.
“Yaya za a ce Ganduje ne shugaban wani abu? Su ne ke sa mu cikin jaridu saboda rikicewa da rudani ya mamaye su. Komai ya tabarbare a fadin kasar nan.”

Martanin NNPP kan sauya shekar Kwankwaso

A wata tattaunawa da Legit.ng, shugaban NNPP na jihar Kano, Dakta Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne kadai zai iya bayyana ko zai sauya sheka ko akasin haka.

Ya ce:

“Tun da labarin daga sama ya zo, ai a nan zai tsaya. Mai girma sakataren dattawan jam'iyya ya ce ba labarin, mai girma sakataren yada labaran jam’iyya ya ce ba labarin, kuma shi ma (Kwankwaso), yana raye bai fada ba.”

Dungurawa ya kara da cewa a matsayinsu na magoya baya, irin wannan rahoto ba zai yadu ba sai dai idan ya fito daga sama ko kuma daga bakin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kansa.

'Ba mu maraba da Kwankwaso,' APC

A wani labarin, kun ji cewa APC reshen Kano ta bayyana cewa maganganun jigon NNPP, Buba Galadima, ba za su sa jam’iyyar ta karɓi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso hannu bibbiyu ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a Kano, Ahmed S. Aruwa, ne ya bayyana hakan yayin da cece-kuce ke ƙara ƙamari kan yiwuwar sauya shekar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC.

A cewar Aruwa, APC ta Kano ba ta maraba da Kwankwaso saboda yadda ba ya biyayya ga tsarin tafiya da shugabanni, wanda zai iya kawo nakasu ga tafiyar jam'iyyar da suka wahaltawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.