Abdullahi Atta, Obasa da Wasu Shugabannin Majalisa 24 da Aka Taba Tsigewa a Najeriya

Abdullahi Atta, Obasa da Wasu Shugabannin Majalisa 24 da Aka Taba Tsigewa a Najeriya

  • Majalisar jihar Legas ta tsige Mudashiru Obasa daga matsayin kakakin majalisar saboda zargin rashin ɗa'a da cin zarafin ofis
  • Bayan tsige Obasa, an zabi Mojisola Miranda, mataimakiyar kakakin, a matsayin sabuwar shugaba don jan ragamar majalisar
  • Legit Hausa ta jero shugabannin majalisar jihohin Najeriya da aka tsige tun daga shekarar 1999 saboda zarge-zarge daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Majalisar dokokin jihar Legas a ranar Litinin, 13 ga Janairu, 2025, ta tsige Mudashiru Obasa daga matsayin kakakin majalisar.

Legit Hausa ta ruwaito cewa ƴan majalisar sun sauke Obasa ne bisa zargin rashin ɗa'a da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Abdullahi Atta da jerin wasu shugabannin majalisar jihohi da aka taba tsigewa a Najeriya
Legit Hausa ta jero wasu shugabannin majalisar jihohi 25 da aka taba tsigewa a Najeriya. Hoto: @nuhu_abok, @RtHonAliyuMdr, @mudashiru_obasa
Asali: Facebook

Haka kuma, 'yan majalisar sun zabi Mojisola Miranda, mataimakiyar kakakin majalisar, a matsayin sabuwar shugabar majalisar, inji rahoton Vangaurd.

Kara karanta wannan

"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta jero wasu daga cikin shugabannin majalisar dokokin jihohin Najeriya da aka tsige tun bayan fara mulkin dimokuradiyya a 1999.

Jihar Edo

1) Victor Edoro:

An tsige shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Victor Edoro, a shekarar 2016 bayan da 'yan majalisa 16 daga cikin 24 na majalisar suka kada kuri'ar tsige shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Elizabeth Ativie ta maye gurbin Vixtyor Edoro, wadda ta zama mace ta farko da ta rike shugabancin majalisar jihar.

2) Frank Okiye:

An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Francis Okiye, a ranar 12 ga Oktobar 2020 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An tsige Okiye bayan wani kuduri daga shugaban masu rinjaye na majalisar, Henry Okhurobo, wanda ya nemi a tsige Okiye bisa zarginsa da amfani da karfin iko ta hanyar da bai dace ba.

Tara daga cikin 10 na 'yan majalisar da suka halarci taron sun sanya hannu kan tsige Francis Okiye.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Jihar Anambra

3) Rita Maduagwu:

An tsige shugabar majalisar Anambra, Hon Rita Maduagwu, bayan kudurin da wani dan majalisa, Hon Ikem Uzoezie, ya gabatar wanda Hon Onyebuchi Offor ya goyi baya.

An tsige Maduagwu ne da karfe 2:00 na yammacin ranar 13 ga Nuwambar 2018, inda 'yan majalisa 22 daga cikin 30 na majalisar suka amince da hakan, kamar yadda THISDAY ta tattaro.

Jihar Neja

4) Adamu Usman:

Majalisar jihar Neja ta tsige kakakinta, Alhaji Adamu Usman, kuma ta zabi Alhaji Isa Kawu a matsayin sabon shugaba a watan Mayun 2015.

An tsige Alhaji Adamu ne bayan da aka hana wasu 'yan majalisar shiga cikin ginin majalisar ta hanyar amfani da rundunar tsaro daga 'yan sanda, SSS da NSCDC.

'Yan majalisa 18 daga cikin 27 sun zabi tsige Usman bisa kudurin da Jacob Maaji (Lavun) ya gabatar wanda Ibrahim Dama (Katcha) ya goyi baya.

Jihar Borno

5) Goni Ali Modu:

Kara karanta wannan

Bincike ya fallasa yadda 'yan majalisa ke tilasta wa jami'o'i biyan rashawa

A watan Fabrairun shekarar 2012, majalisar Borno ta tsige shugabanta, Goni Ali Modu, bisa zarginsa da marawa gwamnatin jihar baya.

An tsige shi ne ta hanyar jefa kuri'ar rashin gamsuwa da shugabancinsa kuma Abdulkareem Lawan Adam ne ya maye gurbinsa.

Jihar Filato

6) Abok Ayuba:

A watan Oktoba, 2021, 16 daga cikin 'yan majalisa 24 na majalisar jihar Filato suka jefa kuri'ar tsige kakakin majalisar, Abok Ayuba, bayan rikici mai tsawo tsakaninsa da tsohon gwamna, Simon Lalong.

A cikin gajeren lokaci, 'yan majalisar suka zabi Sanda Yakubu a matsayin wanda zai maye gurbin Abok Ayuba.

Jihar Gombe

7) Abubakar Ibrahim:

Majalisar dokokin jihar Gombe, a watan Nuwamba, 2020, ta tsige kakakinta, Abubakar Ibrahim, inda Abubakar Luggerewo ya zama sabon shugaba.

An tsige tsohon kakakin bayan jefa kuri'a, inda 'yan majalisa 16 daga cikin 24 na majalisar suka amince da tsige shi.

Jihar Delta

8) Monday Igbuya:

Kara karanta wannan

'Neman gwamna ba zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da aka tsige ya fadi dalilin taso shi a gaba

An tsige Monday Igbuya daga matsayin shugaban majalisar Delta a watan Mayun 2017 bayan da 'yan majalisa 22 suka jefa kuri'ar rashin gamsuwa da mulkinsa.

Sheriff Oborevwori ya maye gurbinsa.

Jihar Katsina

9) Aliyu Sabiu Muduru

A shekarar 2017, majalisar dokokin jihar Katsina ta tsige kakakinta, Aliyu Sabiu Muduru.

'Yan majalisa 23 daga cikin 34 suka goyi bayan jefa kuri'ar rashin gamsuwa da mulkinsa kafin a sanar da tsige shi.

Jihar Imo

10) Paul Emeziem:

Daga cikin 'yan majalisa 27 na majalisar jihar Imo, 19 sun rattaba hannu kan tsige shugaban majalisar, Paul Emeziem a shekarar 2021.

Kennedy Ibeh ne ya maye gurbinsa.

Jihar Ekiti

Kamar Edo, an tsige shugabannin majalisa guda biyu a jihar Ekiti.

11) Gboyega Aribisogan:

A shekarar 2022, 17 daga cikin 'yan majisa 25 na majalisar Ekiti suka sanya hannu wajen tsige Gboyega Aribisogan daga matsayin shugaban majalisar.

12) Kola Oluwawole:

Haka kuma, a watan Oktoba 2018, 'yan majalisa 14 sun rattaba hannu kan tsige shugaban majalisar, Kola Oluwawole da mataimakinsa, Sina Animaun.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sabunta katafaren masallaci, malamai da 'yan siyasa sun hallara

Jihar Taraba

13) Istifanus Gbana:

A shekarar 2013, majalisar dokokin jihar Taraba ta tsige shugabanta, Istifanus Gbana, bayan samun amincewar 'yan majalisa 24.

An maye gurbin Gbana da Haruna Tsokwa wanda daga baya ya rasu cikin wani yanayi mai ban mamaki.

14) Josiah Sabo Kente:

Haka kuma, majalisar Taraba ta tilastawa wani shugabanta Josiah Sabo Kente, ajiye mukaminsa a shekarar 2014.

Jihar Benue

15) Terkimbi Ikyange:

A shekarar 2018, majalisar jihar Benuwai ta zabi Titus Uba a matsayin sabon kakaki.

Wannan ya biyo bayan jefa kuri'ar rashin amincewa da shugabancin Terkimbi Ikyange wanda aka zarga da aikata rashin da'a da cin zarafin ofis.

Jihar Jigawa

16) Idris Garba:

A watan Janairun shekarar 2017, majalisar dokokin jihar Jigawa ta tsige shugabanta, Idris Garba, bisa zarginsa da aikata rashin da'a da cin zarafin ofis.

Takardar tsige shi ta samu sanya hannu 'yan majalisa 25 cikin 30 na majalisar jihar.

Amma a cikin shekaru biyu, a watan Mayun 2019, 'yan majalisar sun cire Isa Idris sannan suka sake zaben Idris Garba a matsayin shugaba.

Kara karanta wannan

Kungiya ta gano sabuwar matsala a rabon harajin VAT, an gargadi gwamnonin Najeriya

Jihar Ondo

17) Bamidele Oloyelogun:

Majalisar jihar Ondo ta tsige shugabanta, Bamidele Oloyelogun, a watan Nuwambar 2018, tare da mataimakinsa, Oladeji Iroju, bisa amincewar 'yan majalisu 26.

An tsige su ne bisa zarginsu da rashin da'a kuma aka zabi wadanda za su maye gurabensu.

Jihar Ebonyi

18) Chukwuma Nwazunku:

A watan Yulin 2014, aka tsige Chukwuma Nwazunku, daga matsayin shugaban majalisar jihar Ebonyi bisa amincewar kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar.

An tsige shi ne bisa zargin rashin kwarewa, aikata rashin da'a, sata, cin hanci da rashawa da kuma dabi'un da za su iya kawo matsala ga tsarin dokokin Najeriya.

Jihar Ogun

19) Olakunle Oluomo:

Bayan wani kuduri da aka gabatar a majalisar Ogun, 18 daga cikin 26 na 'yan majalisar sun tsige shugaban majalisar, Olakunle Oluomo saboda rashin da'a da karkatar da kudade.

ICIR ta ruwaito cewa EFCC ta maka Olakunle a kotu bisa tuhume-tuhume 11 da suka hada da kirkirar takardun bogi, sata da kuma zargin zamba da safarar kudi a watan Satumbar 2022.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur: Mataimakin shugaban majalisa ya fadi alherin da Najeriya ta samu

Jihar Kano

20) Yusuf Falgore:

A watan Disambar 2011, majalisar dokokin jihar Kano ta tsige shugabanta, Yusuf Falgore, kuma ta zabi Gambo Sallau a matsayin sabon kakaki.

21) Abdullahi Atta:

Haka kuma, an tsige wani shugaban majalisar, Abdullahi Atta a watan Yulin 2018.

Kusan 'yan majalisa 27 ne suka sanya hannu kan takardar tsige shi bisa zarginsa da rashin kwarewa, cin hanci da rashin kokarin hada kan majalisar.

Jihar Bayelsa

22) Emmanuel Tonye Isenah:

An ruwaito cewa an tsige shugaban majalisar dokokin jihar Bayelsa, Emmanuel Tonye Isenah, a watan Satumbar 2019 bayan wasu harbe-harbe a cikin ginin majalisar.

Jihar Kebbi

23) Hassan Shalla:

A shekarar 2015, Majalisar dokokin jihar Kebbi ta tsige shugabanta, Hassan Shalla, bayan samun amincewar 'yan majalisa 24 bisa zargin cin amanar aiki da satar kudaden alawus.

24) Isma'il Kamb:

Haka kuma, a shekarar 2021, majalisar ta tsige shugabanta, Isma'il Kamb, da mataimakinsa, Muhammadu Aliyu, bayan 20 daga cikin 24 na 'yan majalisar sun amince da hakan.

Kara karanta wannan

Faransa za ta dauki nauyin tattara bayanan hakar ma'adinai a Najeriya

Jihar Abia

25) Chinedum Orji:

A watan Mayun 2023, aka tsige kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Chinedum Orji, bayan da 18 daga cikin 24 na 'yan majalisar sun sanya hannu wajen cire shi.

Rawar da Tinubu ya taka a tsige Obasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi kokarin sasanta rikicin shugabancin majalisar dokokin Legas yayin hutun Kirsimeti, amma yunkurin ya ci tura.

Fouad Oki, jigon APC, ya bayyana cewa Shugaban kasa Tinubu ya kira taro don warware matsalar, amma rashin biyayya daga bangaren Mudashiru Obasa ya kawo cikas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.