Da duminsa: An tsige kakakin majalisar dokokin Gombe, an nada sabo

Da duminsa: An tsige kakakin majalisar dokokin Gombe, an nada sabo

- Bayan kasa da shekara daya kan kujerar, an tunbuke kakakin majalisa

- Wanda aka cire kafin ya hau ne ya jagoranci cire Kakaki

- Ba tare da bata lokaci ba aka nada sabon Kakaki wanda zai jagoranci majalisar

Mambobi sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Abubakar Ibrahim Kurba, tare da shugaban masu rinjaye a majalisar, Samuel Markus Markwina.

Tsohon mataimakin kakakin, Shuaibu Adamu, wanda aka tsige shekarar nan ne ya gabatar da bukatar tsige Kakakin.

Shuaibu Adamu ya karanto takardar tsige Kakakin bayan mambobi 16 cikin 24 sun rattafa hannu.

An alanta Abubakar Muhammad Luggerewo, mai wakiltar mazabar Akko ta tsakiya, matsayin sabon Kakakin Majalisar, yayinda aka sanar da Yarima Gaule mai wakiltar Kaltungo ta gabas matsayin sabon shugaban masu rinjaye.

KU KARANTA: Buhari ya zabi Farfesa Mahmoud matsayin shugaban INEC, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan

Da duminsa: An tsige kakakin majalisar dokokin Gombe, an nada sabo
Da duminsa: An tsige kakakin majalisar dokokin Gombe, an nada sabo
Asali: UGC

Jawabi ga manema labarai, bulaliyar majalisa, Musa Buba ya yi bayanin cewa an tsige Abubakar Kurba ne saboda yana sabawa dokokin majalisar.

"Tsohon Kakakinmu ya kasance mai karya dokokin majalisa, saboda haka aka yanke shawaran tsigeshi kawai," Musa Buba yace.

Daily Sun ta tattaro cewa gabanin tsige kakakin, an yi rikici yayinda aka tura yan baranda hana wasu mambobi shiga majalisar.

Da kyar suka samu suka shiga kuma suka tsigeshi.

KU KARANTA: Daga karshe, Trump ya fara amincewa ya fadi zabe, ya amince a fara shirye-shiryen mika mulki

A wani labarin, Aishah Isa Ali (Amal), diyar Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Shiekh Isa Ali Pantami ta rasu.

Amal wacce ke da shekaru 13 a duniya ta rasu ne a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamban 2020 kamar yadda Sheikh Pantami ya sanar ta shafinsa na Twitter.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel