Yadda aka tsige Muduru aka sauya shi da Kusada a matsayin kaakakin majalisa

Yadda aka tsige Muduru aka sauya shi da Kusada a matsayin kaakakin majalisa

Kaakakin majalisar dokokin jihar Katsina Aliyu Sabiu Muduru yayi bankwana da kujerar sa a jiya bayan yan majlisu 23 cikin 34 sun yanke yanke shawarar yin awon gaba da shi daga mukaminsa a jiya.

Yadda aka tsige Muduru aka sauya shi da Kusada a matsayin kaakakin majalisa
Muduru da Kusada

A jiyan dai Muduru ne ya jagoranci zaman majalisar, yayin dayake gab da karkare zaman majalisar ne sai dan majalisa Hambali Faruk ya nemi izinin magana, inda ya bayya ma majalisar cewar yan majalisu 23 basu gamsu da kamun ludayinsa ba, don haka ya sauka daha kujerarsa.

Daga nan ne sai aka nada mataimakin kaakaki Shehu Tafoke daya gudanar da zaben sabon Kaakakin, a nan ne fa aka sallami duk wani da ba dan majalisa ba daga farfajiyar majalisar, inda sa’annan ne suka zabi sabon Kaakaki Yahaya Kusada.

KU KARANTA: Sarkin masarautar Borgu, mai murabus ya rasu

Bayan zaben sa ne suka gayyaci yan jaridu don su shaida rantar da sabon Kaakakin, Kusada ya bayyana mamakin zamansa shugaban majalisa, inda yace ikon Allah ne.

Ganin haka ya sanya tsohon dan Kaakakin majalisar tare da wasu su 6 suka fice daga majalisar a fusace, da haka ne Aliyu Sabi’u Muduru ya kawo karshen zangon mukaminsa a majalisar, wanda ya hau yana mai shekaru 34.

Sai dai majiyar mu ta shaida mana “wasu suna ganin tsohon Kaakakin a matsayin dan amshin shata ne ganin yadda yake mu’a’mala da bangaren zartarwar jihar.” Kuma a cewarsu hakan baya yi ma majalisar dadi ko kadam.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng