Da duminsa: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye

Da duminsa: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nu ni da cewa an tsige kakakin majalisar jihar Edo, Hon. Francis Okiye.

An tsige Okiye ne biyo bayan wani kudiri da shugaban masu rinjaye na majalisar Hon. Henry Okhurobo ya gabatar, na bukatar tsige kakakin.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa takardar tsigewar na dauke da sa hannun mambobin majalisar guda 10 da suka halarci zaman majalisar na ranar Litinin.

KARANTA WANNAN: Sakon Atiku Abubakar ga matasan Nigeria bayan rushe rundunar FSARS

Da duminsa: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye
Da duminsa: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye @MobilePunch
Asali: Twitter

Majalisar ta gaggauta rantsar da Marcus Onobun da ke wakiltar mazabar Esan ta Yamma a majalisar dokokin jihar, a matsayin sabon kakakin majalisar.

Rikici a majalisar jihar Edo ya fara ne tun bayan rantsar da shuwagabanninta a cikin wani dare, inda mambobi 9 cikin 24 ne kawai suka halarci taron a ranar 17 ga watan Yunin 2019.

Sai dai 'yan majalisun da ba su halarci wancan taro ba, da kuma jam'iyyar APC, sun nuna rashin amincewarsu da shuwagabannin, tare da bukatar gwamnan jihar ya sa ayi sabon zabe.

KARANTA WANNAN: Malamai sun fatattaki daliban makarantun Abuja, sun hana karatu

Sai dai, wata babbar kotun gwamnatin tarayyada ke a jihar Rivers ta haramtawa Gwamnan tsoma baki a lamarin. Wata kotun kuma ta haramtawa majalisar tarayya sa baki a harkokin majalisar Edo.

Rikicin ya kara tsamari a cikin jam'iyyar APC na jihar tare da kara hura wutar kiyayyar da ke tsakain Obaseki da Adams Oshiomhole, tsohon shugaban APC na kasa.

Ana zargin cewa gwamnan ne ya kitsa korar Oshiomhole daga jam'iyyar APC tun daga matakin gunduma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel