Faransa za Ta Dauki Nauyin Tattara Bayanan Hakar Ma'adinai a Najeriya
- Kasar Faransa ta amince za ta dauki nauyin binciken bayanan ma'adinai na Hukumar Kula da Hakar Ma'adinai ta Najeriya (NGSA)
- Wannan hadin gwiwar ya samo asali ne daga yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a watan Disamban 2024
- Faransa za ta taimaka wajen horaswa, gudanar da bincike, da kuma habaka dakin gwaje-gwajen ma'adinan kasa a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kasar Faransa ta amince da daukar nauyin binciken bayanan hakar ma'adinai na Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Hakar Ma'adinai ta Kasa (NGSA).
Mai ba da shawara na musamman ga Ministan Ma'adanai, Kehinde Bamigbetan ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Asali: Twitter
The Cable ta wallafa cewa Bamigbetan ya ce an tattauna lamarin tsakanin ministan ma'adanai, Dele Alake da jagoran wakilan ma'adinan Faransa, Benjamin Gallezot, yayin wani taro a Saudiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'adinai: Yarjejeniyar Najeriya da Faransa
A ranar 1 ga Disamba 2024, Najeriya da Faransa sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna domin inganta harkokin hakar ma'adinai a kasashen biyu.
Business Day ta rahoto cewa yarjejeniya ta mayar da hankali kan kara habaka manyan sassan masana’antu, tare da magance matsalolin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Bamigbetan ya ce, yayin tattaunawa a Riyadh, Minista Alake ya jinjina wa Gallezot kan gudunmawar da ya bayar domin tabbatar da sanya hannu kan yarjejeniyar.
Sauran batutuwan da aka tattauna
Har ila yau, an tattauna batutuwan da suka hada da gudanar da bincike, tsara dokokin hakar ma'adinai, da aiwatar da wasu tsare-tsare.
Gallezot ya kuma sanar da cewa sashensa yana tantance kamfanonin Faransa da suka nuna sha’awa wajen zuba jari a bangaren hakar ma'adinai na Najeriya.
Ya kuma tabbatar da cewa zai mika sunayen kamfanonin da suka cancanta ga ma’aikatar raya ma’adinai ta Najeriya.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Faransa za ta horar da masana a Najeriya
Wani babban jami’i daga hukumar kula da ma’adinai ta Faransa, Christophe Poinssot ya sanar da cewa Faransa za ta saka Najeriya cikin shirinta na tallafawa kasashen Afrika.
Poinssot ya bayyana cewa sama da masana ma'adanai 1,000 daga Afrika sun amfana daga shirin a cikin shekaru takwas da suka gabata.
A kan haka ya ce Najeriya za ta fara cin gajiyar shirin yayin sabon zagaye da aka tsara, yana tabbatar da cewa za a inganta dakin gwaje-gwajen ma'adinai na Najeriya.
Haka zalika, an amince cewa za a ci gaba da nazartar tsare-tsaren hadin gwiwar a taron shekara-shekara da za a gudanar a watan gobe a Cape Town, Afirka ta Kudu.
Hada kai wajen bunkasa bayanan ma'adinai
A yayin tattaunawar, an mayar da hankali kan hanyoyin da za a gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Faransa domin samun cikakken bayani kan albarkatun ma'adinai.
Ana ganin hakan zai taimaka wajen gina wata babbar ma’adanar bayanai da za ta amfani bangaren masana’antu.
Bamigbetan ya ce, tattaunawar ta maida hankali kan batutuwan da suka shafi hakar ma'adinai mai dorewa, horar da masu sana’ar hakar ma'adinai na hannu, da kuma samar da kudi.
Shettima ya isa kasar Switzerland
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya isa birnin Davos na Switzerland.
Sanata Kashim Shettima zai wakilci Najeriya a Switzerland yayin wani taron tattali arziki da za a gudanar wanda aka saba yinsa shekara shekara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng