Yadda Jami'an Tsaro Suka Kai Samame Yobe, An Gano Makerar Bindigu da Kayan Aikinsu

Yadda Jami'an Tsaro Suka Kai Samame Yobe, An Gano Makerar Bindigu da Kayan Aikinsu

  • Rundunar ‘yan sanda ta gano wata haramtacciyar cibiyar ƙera bindigu da sauran makamai a jihar Yobe
  • An kama mutum bakwai tare da kwato wasu daga cikin bindigun da aka ƙera a sassan makamai daban-daban a samamen
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin faɗaɗa bincike domin gano sauran wuraren ƙera makamai da ake da su ba bisa ƙa’ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe – Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta sanar da gano wata haramtacciyar cibiyar ƙera bindigu a garin Potiskum, inda aka gano wasu da aka riga aka kera.

Rundunar ta bayyana wannan nasara a matsayin wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarinta na daƙile aikata laifuffuka da ayyukan ta’addanci a faɗin jihar Yobe.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan ta'adda, mayaka 50

An gano wurin kera makamai a Yobe
Wasu daga cikin makaman da aka kama a Yobe, Sufeyin Yan sandan Najeriya Hoto: @zagazOlaMakama/Nigeria Police Force
Source: Facebook

Zagazola Makama ya ruwaito ta shafinsa na X cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da kamen

Yobe: Yadda jami’an tsaro suka kai samame

Leadership ta wallafa cewa jami’an tsaro sun tattara bayanan da suka nuna cewa ana gudanar da haramtacciyar sana’ar ƙera makamai a wani wajen maƙera da ke Tasha Adua a kan titin Danchuwa da ke Potiskum.

Bayan isa wurin, jami’an sun cafke mutum bakwai tare da kwato kayayyaki da dama da ake zargin ana amfani da su wajen ƙera bindigun.

Daga cikin kayayyakin da aka samu akwai bindigu biyu da aka ƙera, bututun bindiga guda 24, tsofaffin bindigu da ba sa aiki huɗu, na’urar goga ƙarfe ɗaya da sauran miyagun makamai.

Rundunar ta ce wannan kamen ya nuna yadda take ƙara zage damtse wajen hana yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma dakile ayyukan masu aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Fusatattun mutanen gari sun hallaka dan acaba kan 'karyar' harin yan bindiga

Ƴan sanda na fadada bincike a Yobe

‘Yan sanda sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan waɗanda aka kama domin gano sauran mutanen da suke haɗa kai da su, masu sayen makaman da ake ƙerawa da kuma manufar amfani da su.

An kama mutane da ake zargin na da alaka da gidan kera makamai a Yobe
Taswirar jihar Yobe, mai fama da ayyukan Yan ta'adda a Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya umarci jami’an da ke kula da shari’ar su ƙara ƙaimi wajen bincike domin gano sauran cibiyoyin ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a yankin.

Ya kuma buƙaci a tantance irin barazanar tsaro da irin waɗannan ayyuka ke haifarwa ga al’umma jihar da kewaye.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da kada su bari a yi amfani da gidajensu ko wurarensu wajen gudanar da haramtattun ayyuka, musamman waɗanda suka shafi ƙera makamai masu haɗari.

Haka kuma ta shawarci mazauna jihar da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargin yana da alaƙa da laifi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Jam'iyyar APC ta bukaci Gwamna Seyi Makinde ya yi murabus

An Kama ɗan sa kai a Yobe

A baya, mun kawo labarin cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani dan sa-kai da ake zargi da yi wa mayakan ISWAP leken asiri tare da taimakonsu a jihar Yobe.

Ana zargin mutumin na hulɗa da ‘yan ta’adda tare da ba su bayanai a asirce wanda ke kassara kokarin jami'an tsaro wajen yakar ta'addanci a jihar Yobe da ma yankin baki daya.

Sojoji sun ce ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin a hedikwatarsu bayan an yi amfani da dabaru wajen cafke mutumin, sannan za a ci gaba da tatsar bayanai a kan al'amarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng