Omo Agege: Jam'iyyar APC Ta Rasa Wani Babban Jigo Ana Tunkarar Zabukan 2027

Omo Agege: Jam'iyyar APC Ta Rasa Wani Babban Jigo Ana Tunkarar Zabukan 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya fice daga jam’iyyar APC bayan rikice-rikicen siyasa a Delta
  • Omo-Agege ya ce ba zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ba zai iya kare muradun mutanen mazabar shiyyar Delta ta Tsakiya ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka ruwaito cewa Omo-Agege ya gaza samun tikitin takarar kujerar sanata a zaben fitar da gwani na APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Delta - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Omo-Agege ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Areh ya fitar.

Ovie Omo-Agege ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sanata Ovie Omo-Agege
Source: Facebook

Dalilin ficewar Omo-Agege daga APC

Sanarwar wacce aka wallafa a shafin Omo-Agege na facebook, ta ce tsohon sanatan ya fice daga APC ne bayan tattaunawa da magoya bayansa.

Kara karanta wannan

'Yan dabar siyasa sun farmaki sanatar Abuja, sun tarwatsa taron jam'iyyar ADC

Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban majalisar ya ce bai yanke wannan shawara ba sai da ya duba sababbin rikice-rikicen siyasa da suka kunno kai a APC reshen jihar Delta.

Omo-Agege ya ce manufofinsa na siyasa da muradun al’ummar Delta ta Tsakiya sun fi dacewa a wata jam'iyyar amma ba APC ba.

Ya bayyana cewa ba zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ba zai iya kare muradun mutanensa yadda ya kamata ba.

Omo-Agege ya yi godiya ga APC

Tsohon dan majalisar dattawan ya ce:

“Bayan nazarin abubuwan da ke faruwa a APC a Delta da kuma tuntuba da magoya bayana, na fahimci cewa muraduna da na al’ummata sun fi dacewa a wajen jam’iyyar.”

Ya kuma bukaci a cire sunansa daga dukkan bayanan mambobin APC da kundin sadarwar jam’iyyar, in ji rahoton Punch.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya gode wa APC bisa damar da ta ba shi na zama mataimakin shugaban majalisar dattawa ta tara.

Sai dai ya jaddada cewa zai ci gaba da fafutukar kawo cigaba ga Delta ta Tsakiya, jihar Delta da Najeriya baki ɗaya ko da kuwa a wajen APC.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Sanarwar ta nuna cewa murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take tun daga ranar 22 ga watan Mayun 2026.

Sanata Omo-Agege ya fice daga APC ne bayan ya sha kasa a zaben fitar da gwani.
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Omo-Agege ya sha kaye a zaben fidda gwani

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Omo-Agege ya tsaya takarar neman tikitin APC a Delta Central amma ya sha kaye a hannun Sanata Ede Dafinone.

Dafinone ya samu kuri’u 116,252 yayin da Omo-Agege ya samu kuri’u 3,643 kacal a kananan hukumomi takwas na yankin.

Tun farko Omo-Agege ya taba zama sanata na wa’adi biyu kafin daga bisani ya tsaya takarar gwamnan jihar Delta a 2023 amma ya sha kaye a hannun Sheriff Oborevwori.

Pantami ya fice daga jam'iyyar APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Isa Ali Pantami ya sauya sheka daga APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Gombe bayan rasa rikitin takara.

Tsohon ministan na sadarwa ya kuma samu tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2027 karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP.

Masu ruwa da tsakin PDP a Gombe ne suka tabbatar da Pantami a matsayin dan takarar gwamna a wani taro da aka gudanar yau Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com