An Samu Hirar Trump da Jami'ansa da ke Nuna Fargabar Yaki da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa wasu manyan mataimakansa a sirrance cewa ba zai cigaba da musayar wuta da Iran a fagen daga ba
- Duk da yawaitar arangama a yankin, jami’an sun ce yarjejeniyar dakatar da kai hare-haren sama da aka shafe makonni ana aiwatarwa tana nan daram
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ke cewa sun kusa cimma yarjejeniya da Iran domin kawo karshen yakin da suka fara a Fabrairun 2026 gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rashin goyon Donald Trump kan sake kunna wutar yaki da Iran ya kara bayyyana a wata hirar sirri da ya yi da jami'ansa.
Rahotanni sun ce Trump ya gindaya sharadi kan yiwuwar sake kai hare-hare kan Iran, inda ya sanar da manyan mataimakansa cewa Amurka ba za ta sake kai farmaki ba sai idan an kashe sojojinta.

Source: Getty Images
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa wannan sabon mataki na gwamnati yana nuna kokarin rage tashin hankali a yankin a Gabas ta Tsakiya.
Matsayar Trump kan yakin Iran
A cewar wasu majiyoyi daga cikin gwamnati, sakonnin sirri da Trump ya aika wa mukarrabansa sun nuna cewa yana son kauce wa sake fadawa wani cikakken yakin soji a Gabas ta Tsakiya.
Ta hanyar danganta duk wani martanin soji na gaba da yiwuwar mutuwar sojojin Amurka, Trump na kokarin fayyace iyakar abin da Iran ba za ta ketare ba.
Wannan matakin na nuna takatsantsan ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa a yankin, inda Washington ke nuna cewa za ta iya jure wasu matsalolin siyasa da tsaro daga Iran.
Baya ga batun soji, rahotanni sun ce Trump na mayar da hankali wajen warware matsalar shirin nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa maimakon amfani da karfin soji.
Wani jami’in Amurka ya shaida wa Roya News cewa shugaban kasar ya fi son a samu cikakken rushe shirin nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya maimakon yaki.
Iran ta yi gargadi kan Lebanon
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya gargadi cewa kai hari birnin Beirut zai iya haddasa sake barkewar yakin Gabas ta Tsakiya gaba daya, yayin da Isra’ila ke ci gaba da yakin da take yi da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.
Iran ta sha nanata cewa duk wata yarjejeniya da za ta kawo karshen yakin da ke gudana a yankin dole ne ta hada da dakatar da fada a Lebanon.
Ya ce:
“Makomar yakin da ke tsakanin Iran da Yahudawan Isra’ila da kuma Amurkawa tana da alaka kai tsaye da yakin da ake yi a Lebanon.”

Source: Getty Images
Majalisa ta takawa Trump burki
A wani labarin, kun ji cewa majalisar wakilan Amurka ta amince da wani kuduri da ke neman hana shugaba Donald Trump daukar karin matakin soji kan Iran ba tare da izini ba.
Kudurin ya samu rinjaye da kuri’u 215 cikin 208 bayan wasu ‘yan jam’iyyar Republican guda hudu sun hada kai da ‘yan Democrat wajen nuna rashin amincewarsu da yakin.
Wannan shi ne karo na hudu da majalisar ke kokarin takaita ikon Trump na kaddamar da yaki, inda masu adawa da matakin ke cewa ba a samu sahalewar majalisa ba.
Asali: Legit.ng

