Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato

Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato

  • Majalisar dokokin jihar Filato ta tsige shugaban majalisar, Honorabul Abok Ayuba Nuhu
  • Rahotanni sun bayyana cewa mambobin majalisar 16 cikin 24 ne suka kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisan
  • Bayan tunɓuke shi, majalisar ta kuma amince da maye gurbinsa da Honorabul Sanda Yakubu

Plateau - Majalisar dokokin jihar Filao ta tsige kakakinta, Honorabul Abok Ayuba Nuhu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa an maye tsohon kakakin da Honorabul Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana, karamar hukumar Bassa, jihar Filato.

Mambobin majalisa 16 cikin 24 na majalisar dokokin ne suka kada kuri'ar amince wa da tsige shugaban nasu a zaman majalisa na yau Alhamis.

Abok Ayuba Nuhu
Da Dumi-Dumi: Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato Hoto: @The state of Plateau
Asali: Facebook

Channels TV ta rahoto cewa Mambobin majalisa na jam'iyyar APC mai mulki ne suka tsige shugaban da sanyin safiyar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby"

Legit.ng Hausa ta gano cewa an tsaurara matakan tsaro a hanyar shiga majalisar, domin sai da jami'an tsaro suka raka mambobin zuwa cikin zauren.

Hotunan yadda aka tsaurara tsaro

Tsaro a Majalisar Filato
Da Dumi-Dumi: Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin majalisan Filato
Karin bayani da Hotuna: Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata a tsige shugaban majalisar dokokin Filato Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jami'an tsaro s Filato
Da Dumi-Dumi: Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Tun da misalin ƙarfe 5:30 mambobin majalisar harda na jam'iyyar hamayya suka mamaye zauren majalisar.

An yi musayar yawu tsakanin ɓangarorin biyu na PDP da APC yayin da aka gabatar da kudirin tsige kakakin majlisar.

Mambobin jam'iyyar adawa PDP, waɗanda ke nuna goyon bayansu ga shugaban majalisar, sun yi kokarin hana tsige shi ta hanyar ɗauke sandar majalisa.

Amma mambobin APC, waɗanda suke da mafi rinjaye a majalisar, sun kwace sandar tare da maida ta inda take, kuma aka cigaba da bin matakan tsigewan.

Kara karanta wannan

EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta

Meyasa aka tsige shi?

Rahotanni sun bayyana cewa na fara takun saka tsakanin kakakin majalisa da kuma Gwamnan jihar, Simon Lalong, bayan harin Yelwan Zagam.

Bayan kai harin, kakakin majalisar ya fara sukar gwamna a bayyane, kuma ya daina halartar ayyukan gwamnatin jihar.

A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace yanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya.

Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel