Majalisa Ta Fara Ɗaukar Mataki kan Rashin Tsaro, Ana Son Samar da Yan Sandan Jihohi
- Majalisar Dattawa ta fara shirye-shiryen sauya kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi saboda matsalar tsaro
- Sanatoci sun ce za su gaggauta daukar matakan doka don tallafa wa yaki da matsalar tsaro a Najeriya bayan sace wasu bayin Allah
- Yunkurin ya biyo bayan karuwar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma sace dalibai a sassan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta fara aiwatar da matakan kundin tsarin mulki da za su kai ga kafa rundunar ‘yan sandan jihohi domin karfafa tsaro da dakile ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yada labarai da harkokin jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana hakan a ranar Laraba 4 ga watan Yuni, 2026.

Source: Facebook
A hira da ya yi da jaridar Punch, majalisar dattawa ta shirya tsaf domin fara matakan da suka dace na sauya kundin tsarin mulki ba tare da bata lokaci ba.
Sanatoci sun fusata kan rashin tsaro
Sanata Yemi Adaramodu ya ce sanatocin na son tallafawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wajen magance kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara a fadin Najeriya.
Adaramodu ya bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da cewa an samar da dukkannin goyon bayan doka da ake bukata domin ganin an kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, tare da kara tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan sabon yunkuri na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalar tsaro, musamman bayan harin da wasu mahara suka kai makarantu uku a yankunan Ahoro-Esinle da Yawota da ke jihar Oyo.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da dalibai da malamai da dama, lamarin da ya jefa iyalai cikin tashin hankali tare da tayar da kura a fadin kasar.
Sanatoci sun yi Allah wadai da haɗin Oyo
Bayan dawowar majalisar daga hutun Sallah a ranar Talata, sanatoci sun yi Allah-wadai da harin tare da tsayawa na minti guda domin karrama malamai biyu da suka rasa rayukansu sakamakon lamarin.

Source: Facebook
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana harin a matsayin babban bala’i da ya shafi makomar Najeriya.
Ya ce hare-haren da ake kai wa makarantu na nuna bukatar daukar karin matakan tsaro domin kare al’ummomi masu rauni da kuma cibiyoyin ilimi.
Masu goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi sun dade suna jaddada cewa tsarin zai taimaka wajen tattara bayanan sirri cikin sauki.
Majalisa za ta ceto sanatocin APC
A baya, mun wallafa cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan sanatocin da suka gaza samun tikitin jam’iyyunsu a zabukan fitar da gwani na baya-bayan nan.
Akpabio, wanda ya samu tikitin jam’iyyar APC ya ce shugabancin majalisar dattawa ya yi tsammanin sanatoci kaɗan ne kawai za su rasa damar sake tsayawa takara a zaben 2027.
Ya bayyana cewa shugabancin majalisar na nazarin hanyoyin da za a bi domin magance wasu daga cikin sakamakon zabukan fitar da gwanin tare da taimaka wa sanatocin.
Asali: Legit.ng

