Yan sanda sun rufe majalisar dokokin jihar Anambra
Bayan hargitsin da ya faru a kofar majalisar dokokin jihar Anambra a ranar lhamis, 15 ga watan Nuwamba, rundunar yan sandan jihar sun ce sun rufe ginin majalisar har sai baba ya gani.
A wata sanrwa daga kakakin rundunar yan sandan, Haruna Mohammed a ranar Juma’a, 16 ga watan Nuwamba yace sun rufe ginin ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
A ranar Alhamis ne yan sanda suka harba wa wata yar majalisa, ma’aikata da magoya bayan kungiyoyin majalisar jihar barkonon tsohuwa yayinda rikici ya zafafa kan shugabancin majalisar.

Asali: UGC
An samu rabuwar kai a majalisar a ranar Talata kan zargin tsige kakakin majalisar, Rita Maduagwu da wasu mambobi 20 cikin 30 suka yi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta rage yawan shekarun da Jolly Nyame zai yi a gidan yari zuwa shekara 12
An tattaro cewa an maye gubinta da Ikem Uzoezie wanda ke wakiltan mazabar Aguata II.
Amma da taimakon wasu jami’an jihar ta sake samun shiga majalisar sannan ta yi zama da mambobin majalisar 11.
Ta kuma bayyana tsigeta a matsayin ba bisa ka’ida ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng