Manyan dalilai guda 3 da suka sabbaba tsige Kaakakin majalisar jihar Kano sun bayyana
A ranar Litinin, 30 ga watan Yuli ne yayan majalisar Dokokin jihar Kano suka tsige shugabansu, wato Kaakakin majalisar, Abdullahi Ata tare da wasu mukarrabansa guda biyu, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.
Dan majalisa mai wakiltar Warawa Labaran Madari ne ya bayyana bukatar tsige Kaakakin, inda ya samu goyon dan majalisar PDP daya tilo dake majalisar, Abdullahi Muhammed, tare da sauran yan majalisu 27 cikin 44, kuma nan take yan majalisar suka maye gurbinsa da tsohon Kaakakin majalisar da suka yi wa juyin mulki, Kabiru Rurum.
KU KARANTA: Nahiyar Turai ta baiwa El-Rufai tallafin naira biliyan 4.2 don kammala wani muhimmin aiki
Sai dai bayanai na baya bayan nan dake fitowa sun bayyana wasu zunubbai guda uku da tsohon Kaakaki Atta yake aikatawa, da suka hada da zargin cin hanci da rashawa, zuwa bakin aiki latti da kuma rashin tafiya tare da sauran jigogin majalisar akan ayyukan majalisa.
Wasu sahihan rahotanni sun bayyana cewa tun a ranar 15 ga watan Mayu yan majalisun suka yi kokarin tumbuke Atta daga mukaminsa, amma sai gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya shiga tsakaninsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng