An Shiga Tashin Hankali da Jirgi Dauke da Mutane Sama da 300 Ya Yi Hatsari a Najeriya

An Shiga Tashin Hankali da Jirgi Dauke da Mutane Sama da 300 Ya Yi Hatsari a Najeriya

  • Akalla mutane 30 ake fargabar sun mutu, yayin da wasu 300 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a Jihar Bayelsa
  • Lamarin ya faru ne kusa da kauyen Oweikorogha a Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw, lokacin da fasinjojin ke tafiya zuwa wurin jana’iza a Ukubie
  • Rahotanni sun ce jirgin ya cika fiye da ƙima, yayin da jami’an tsaro da masu aikin ceto ke ci gaba da neman waɗanda suka tsira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa, Nigeria - akalla mutane 30 sun mutu, yayin da wasu 300 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da masu zuwa jana’iza a Ukubie ya kife a jihar Bayelsa.

Jirgin ruwan, wanda aka tabbatar yana dauke da mutane sama da 300 ya yi hatsari ne a kusa da kauyen Oweikorogha, a Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw ta Jihar Bayelsa, ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Ayarin Shugaba Tinubu ya jefa mutane cikin babbar matsala ta taawon lokaci a Abuja

Jirgin ruwa.
Yadda wani jirgin ruwa makare da mutane ya yi hatsari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa bikin jana’iza a al’ummar Ukubie da ke Southern Ijaw ne lokacin da mummunan lamarin ya faru.

Abin da ya jawo kifewar jirgin ruwa

An ce mutanen sun yi amfani da wani jirgin ruwa mai faɗi (barge) domin zuwa jana’izar, amma jirgin ya cika fiye da ƙima kafin ya kife.

Mazauna yankin sun shaida cewa jirgin ya nutse ne jim kaɗan bayan ya wuce garin Oweikorogha, inda fasinjojin suka faɗa cikin ruwa, wasu da dama kuma suka ɓace.

A cewarsu, har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin mutanen da ke cikin jirgin da kuma waɗanda suka ɓace ba. Sai dai ana ci gaba da aikin ceto, inda mazauna yankin suka haɗa kai wajen neman waɗanda suka tsira.

Lamarin ya jefa al’ummomin Ukubie da Oweikorogha cikin jimami, yayin da iyalai ke jiran samun labarin ’yan uwansu.

Fasinjoji sama da 300 sun ɓace

Kara karanta wannan

2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna

Wata majiya daga yankin, wadda ta kasance a bakin jirgin ruwa lokacin da ake loda fasinjoji, ta ce ana fargabar sama da mutane 30 sun mutu, yayin da wasu 300 suka ɓace.

Ta ce wadanda suka iya ruwa na yankin da sauran mutanen masu kawo taimako sun shiga cikin tawagar masu aikin ceto.

Majiyar ta ce rahotanni sun nuna cewa jirgin ya cika fiye da ƙima, sannan ya kife jim kaɗan bayan wucewar ta garin Oweikorogha.

Rahotanni sun nuna cewa wasu fasinjoji sun ba da shawarar a tsaya a Oweikorogha domin rage cunkoson da ke cikin jirgin, saboda yawan mutanen da ke cikinsa amma ba a bi wannan shawara ba.

Bayelsa.
Taswirar jihar Bayelsa da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan sanda sun kai dauki

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu bai tabbatar da adadin waɗanda abin ya rutsa da su ba.

"Lallai lamarin ya faru. Kwamishinan ’yan sanda ya tura ’yan sandan ruwa da kuma jami’in ’yan sanda na yankin da abin ya shafa, ƙarƙashin sashen Oporoma, domin su jagoranci aikin ceto a wurin," in ji shi.

Jirgin ruwa ya halaka mutum 30

Kara karanta wannan

Mutane suna shan wahala a kasa, Tinubu ya shirya kawo sauki ta hanyar sufuri

Kun ji cewa hukumar SEMA ta jihar Benuwai ta tabbatar da mutuwar fasinjoji sama da 30 a hatsarin jirgin ruwa a mashigar Buruku.

Gwamnatin Jihar Benue ta dakatar da ayyukan reshen Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Ruwa ta Najeriya (NUMW) na mashigar Buruku nan take sakamakon hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262