Dan Najeriya Ya Fara Garkuwa da Mutane a Amurka, 'Yan Sanda na Neman Shi
- Rundunar ’yan sandan Philadelphia ta Amurka ta ayyana Olukayode J. Taiwo, ɗan 'yar jarida Kemi Olunloyo, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo
- Ana zargin Taiwo da yin garkuwa da wata mata da bindiga, sannan ya yi harbi a gidanta a wani lamari na daban duk a kasar Amurka
- Rahotanni sun nuna cewa dakarun ’yan sandan Amurka sun ce suna zargin matashin da aikata laifukan biyu, waɗanda suka shafi mace ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Philadelphia, Amurka – Rundunar ’yan sandan Philadelphia da ke Amurka ta ayyana Olukayode J. Taiwo, ɗan fitacciyar ’yar jaridar Najeriya Kemi Olunloyo, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin sace wata mata da bindiga da kuma harbi.
Taiwo, wanda aka fi sani da Rick KJT, ya shiga jerin waɗanda ’yan sanda ke nema bayan bincike ya danganta shi da wasu hare-hare guda biyu da aka kai wa mace ɗaya.

Source: Facebook
Yadda aka yi garkuwa da matar
A cewar rundunar ’yan sandan kamar yadda Tribune ta rahoto, lamarin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar 2 ga Nuwamba, 2026.
An ce wanda ake zargin ya yi garkuwa da matar ne da bindiga a unguwar West Seybert Street, da ke yankin North Philadelphia.
An sake kai mata hari da harbi
Masu bincike sun ce a ranar 15 ga Nuwamba, 2026, Taiwo ya sake harba bindiga har sau biyu a inda matar take da kuma gidanta.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Rugby Street, da ke unguwar Cedarbrook a birnin Philadelphia.
Sai dai rundunar ’yan sandan ba ta bayyana halin da matar take ciki ba, ko kuma abin da ya jawo rikicin da ake zargin ya faru tsakaninta da wanda ake nema.
Motar da ake zargin yake amfani da ita
’Yan sanda sun ce suna zargin Taiwo na iya amfani da motar Honda Accord mai launin azurfa ko toka, wadda aka ruwaito cewa samfurin shekarar 2026 ce.
Rahotanni sun nuna cewa motar tana da lambar rajistar jihar Pennsylvania mai lamba H900330.
Wasu bayanai sun nuna cewa an haifi Taiwo ne a Amurka, amma ya koma Najeriya tare da mahaifiyarsa bayan da aka tasa keyarta daga kasar.

Source: Getty Images
Daga bisani, ya koma Amurka bayan kammala karatunsa na sakandare a Najeriya.
Rundunar ’yan sandan Philadelphia ta yi kira ga duk wanda ke da bayanin inda yake ko zai taimaka wajen kama shi da ya tuntubi jami’anta ta lambar waya 215-686-TIPS (8477).
Amurka na tallafawa Najeriya
A wani labarin, mun rahoto cewa Ministan tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa sojojin Najeriya na samun bayanan sirri kai tsaye da taimakon tauraron ɗan adam daga Amurka domin gano shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda.
Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, inda ya ce sojojin Najeriya sun kashe wasu shugabannin ’yan ta’adda da ’yan bindiga a hare-haren da suka kai da daddare.
Ya ƙara da cewa sojojin na gudanar da hare-hare kusan kullum, inda taimakon hotunan tauraron ɗan adam, musayar bayanan sirri da horo daga Amurka suka inganta ƙarfinsu wajen gano wuraren da ’yan ta’addan suke da kai musu farmaki.
Asali: Legit.ng

