Za a Dawo da Man Fetur N200 idan Dan Takarar SDP Ya Lashe Zabe
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin kawo karshen Boko Haram cikin wata uku idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027
- Adebayo ya kuma yi alkawarin rage farashin litar fetur zuwa N200 tare da bunkasa amfani da motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG
- Ya bayyana wadannan alkawura ne a wajen gangamin yakin neman zabensa a Yola, jihar Adamawa, inda ya bukaci al’umma su kada kuri’unsu ga jam’iyyar SDP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi alkawarin kawo karshen hare-haren Boko Haram cikin wata uku bayan kama mulki idan ya lashe zaben 2027.
Adebayo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Yola, jihar Adamawa, inda ya bukaci mazauna yankin su zabi SDP tare da kifar da jam’iyyar APC mai mulki a zaben da ke tafe.

Source: UGC
Punch ta wallafa cewa kakakin yakin neman zaben SDP, Mark Adebayo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Za a kawo karshen Boko Haram
Da yake jawabi tare da dan takarar gwamnan jihar Adamawa na SDP, Dr Christopher Nathaniel, Adebayo ya dora alhakin ci gaba da matsalar tsaro a Arewa maso Gabas kan rashin kyakkyawan shugabanci.
Ya koka kan yadda hare-haren Boko Haram suka yi sanadin asarar rayuka da kuma tilasta wa al'ummomi da dama barin gidajensu, inda wasu suka shafe shekaru suna rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ya ce akwai yara da aka haifa kuma suka taso a sansanonin ‘yan gudun hijira, amma har yanzu babu wani dan siyasa da ya yi cikakken bayani kan halin da suke ciki.
Adebayo ya tuna da yadda sojoji suka yi fafutukar kwato wasu garuruwa kamar Mubi, Madagali, Michika, Gwoza da Bama daga hannun ‘yan ta’adda, yana mai cewa gwamnatocin baya sun gaza samar da mafita ta dindindin.
Ya ce:
“Cikin wata uku da samun mulki, za mu kawo karshen Boko Haram. Ni da mataimakina, Usman Bugaje, ba mu da wata alaka da su.”
Litar fetur za ta dawo N200
Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin rage farashin man fetur zuwa N200 kan kowace lita idan ya zama shugaban kasa.
Ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa amfani da motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG domin rage kudin sufuri ga ‘yan Najeriya.
Adebayo ya ce zai mayar da hankali kan tsaro, samar da abinci mai saukin kudi, ilimi kyauta, ingantaccen kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.

Source: Getty Images
Ya kuma soki Shugaba Bola Tinubu kan neman karin lokaci domin magance matsalolin tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa kasar na bukatar sauyin shugabanci da gwamnati mai daukar alhakin ayyukanta ga al'umma.
Atiku zai maido tallafin mai
A wani labarin, mun rahoto cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake jaddada alkawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce dawo da tallafin zai taimaka wajen rage wa ‘yan Najeriya radadin tsadar rayuwa tare da saukaka musu samun man fetur.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar a ranar Litinin, tare da wani bidiyon yakin neman zabe da ya yi bayani kan tsarin tallafin da yake son dawo da shi.
Asali: Legit.ng


