Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 13 a Abuja, Sun Nemi N900m Kudin Fansa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 13 a Abuja, Sun Nemi N900m Kudin Fansa

  • Akalla mutane 13 ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai kauyen Piko, karamar hukumar Bwari, da ke Abuja
  • An ruwaito cewa 'yan bindigar sun nemi Naira miliyan 900 a matsayin kudin fansar mutanen da suka tare kafin su sako su
  • An gano 'yan bindigar sun afkawa garin Piko da sanyin safiyar Lahadi inda suka shafe awa daya suna cin karensu ba babbaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wasu ‘yan bindiga sun sake kai farmaki wani kauyen karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi garkuwa da mutane 13.

Harin da aka kai wa al’ummar Piko na zuwa ne kasa da mako guda bayan irin wannan farmakin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Bmuko da ke yankin Bwari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun kashe mutane da dama

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Bwari, babban birnin tarayya Abuja
'Yan bindiga sun nemi N900m kudin fansar mutane 13 da suka sace a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun afkawa garin Piko da sanyin safiyar Lahadi inda suka dauki sama da awa daya suna cin karensu ba babbaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan bindigar sun nemi N900m" - Majiya

Wani mazaunin garin ya shaida cewa, Madakin Piko, Cif John Jatau, ya tabbatar da yin garkuwa da mazauna yankin 10 da wasu Fulani makiyaya hudu a yayin harin.

Ya bayyana cewa mutum daya ya tsere daga cikin makiyayan hudu daga hannun masu garkuwa da mutane, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yayin da ya ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 900, ya kuma bayyana sunayen mutanen da aka sace daga garin.

Jerin wadanda aka yi garkuwa da su

A cewarsa, an yi garkuwa da wadannan mutane daga cikin garin kuma har yanzu suna tsare a hannun wadanda suka sace su:

Kara karanta wannan

Yakin Isra'ila kan Hamas: Sojin Isra'ila sun yiwa Falasdinawa 5 kisan gilla a kogin Jordan

Nuhu anyiwoyi, Emmanuel Nuhu, Danjuma Ali, Parisa Numa, Ezekiel Jatau, Shekwosa Ezekiel, Roseline Samuel, Salome Jacob, Abyelo Ezra, da Ezra Male.

“Madakin Piko ya sanar da ni cewa sun yi waya kuma sun ce suna bukatar kudin fansa har Naira miliyan 900."

- A cewar majiyar.

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen Ambe da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

A yayin wannan farmakin, 'yan bindigar sun kashe mutane shida tare da raunata wasu takwas yayin da rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce an kama dan bindiga daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel