An Amsa Tambayoyin da Mutane ke Yi kan Neman Tallafin N100,000 na Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu kudin da mutum zai biya kafin neman tallafin Naira 100,000 karkashin shirin NFSP
- Ta ce tallafin kyauta ne ba bashi ba, kuma ta gargadi ’yan Najeriya da su guji biyan masu ikirarin za su taimaka masu wajen samun gurbin cin gajiyar shirin
- An bayyana cewa ’yan Najeriya masu shekaru 18 zuwa 65 da ke da lambar NIN za su iya neman tallafin, amma cika sharuda ba ya nufin za a zabe su kai tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar gudanarwar shirin tallafin iyalai na Najeriya (NFSP) ta bayyana sharuddan samun tallafin N100,000 da yadda masu sha’awar neman tallafin za su iya yin rajista.
A cewar bayanin da hukumar ta fitar, shirin na karkashin Ma’aikatar Matasa ta Tarayya ne, kuma an tsara shi ne domin tallafa wa iyalai masu karamin karfi da ke fama da matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayan abinci.

Source: Facebook
Shafin Renewed Hope UK a X ya ce ya kamata masu neman tallafin su tabbatar da sahihancin shafin da za su shiga kafin mika bayanansu masu muhimmanci.
Ba a biyan kudi don neman tallafin
Hukumar gudanarwar shirin ta bayyana cewa babu kudin rajista ko na sarrafawa da mutum zai biya kafin neman tallafin ko karbar Naira 100,000.
Ta jaddada cewa tallafin kyauta ne, ba bashi ba, don haka babu bukatar biyan wani mutum ko kamfani domin samun damar cin gajiyarsa.
Hukumar ta kuma gargadi ’yan Najeriya da su guji masu ikirarin za su iya tabbatar musu da samun tallafin ko sanya sunayensu cikin jerin wadanda za su amfana.
Sharudan samun tallafin N100,000
A cewar hukumar, wadanda ke son neman tallafin dole ne su cika wadannan sharuda:
- Kasancewa dan Najeriya da aka haifa a kasar
- Kasancewa tsakanin shekaru 18 zuwa 65 a lokacin rajista.
- Samun ingantacciyar lambar shaidar dan kasa (NIN) wadda za a tantance ta hannun Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC).
- Kasancewa cikin iyalai masu karamin karfi ko wadanda ke fuskantar matsin tattalin arziki.
Hukumar ta bayyana cewa cika wadannan sharuda ba ya tabbatar da cewa za a zabi mutum, domin za a tantance halin tattalin arzikin iyalansa da matakin bukatarsa kafin amincewa da tallafin.
Gargadi kan 'yan damfara
Hukumar ta bukaci ’yan Najeriya da kada su biya wani mutum ko wakili da ke ikirarin zai taimaka musu su samu tallafin ko ya saka sunayensu cikin jerin wadanda za su amfana.
Ta kuma shawarci masu neman tallafin da kada su bayar da bayanan sirri kamar lambar sirrin katin ATM, kalmar sirrin asusun banki ko lambar OTP ga wani mutum.

Source: Facebook
Bayanan shirin sun bayar da adireshin imel din help@nfsp.ng domin neman karin bayani, amma ya kamata a tabbatar da sahihancin wannan adireshi da sauran hanyoyin sadarwar shirin kafin aika bayanan sirri.
Magana kan bashin N100m
A wani labarin, mun rahoto cewa ’yan Najeriya za su iya neman bashin sayen gida har Naira miliyan 100 karkashin shirin rancen kudi na MOFI Fund na gwamnatin tarayya.
An bayyana cewa shirin na bayar da bashin ne kan kudin ruwa na kashi 9.75 a shekara, tare da wa’adin biya har zuwa shekaru 20.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce masu neman bashin za su iya fara da biyan kashi 10 na kudin gidan da suke son saya su biya sauran daga baya.
Asali: Legit.ng