Kotu Ta Kawo Cikas ga Yunkurin Atiku na Neman Hana Tinubu Yin Takara a 2027

Kotu Ta Kawo Cikas ga Yunkurin Atiku na Neman Hana Tinubu Yin Takara a 2027

  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da wata bukatar Atiku ya gabatar kan shari'ar da ya shigar da mai girma Bola Tinubu
  • Kotun ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi kwanaki 14 kacal domin gabatar da hujjoji a shari’o’in da suka shafi zaɓe
  • Kotun ta sanya ranar 2 ga Disamba domin sauraron ƙarar da Atiku da ADC suka shigar don neman hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Atiku Abubakar, na gabatar da sababbin hujjoji a ƙarar da ya shigar domin neman hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ƙarar ta shafi zargin cewa Tinubu ya yi amfani da takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC ta bogi.

Kara karanta wannan

APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

Atiku ya kai karar Tinubu
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamban 2026 inda ya ce bukatar Atiku ta saɓa wa sashe na 285(9) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, cewar rahoton jaridar The Punch.

Wannan sashe ya tanadi wa’adin kwanaki 14 domin shigar da ƙara da gabatar da hujjoji a shari’o’in da suka shafi zaɓe kafin gudanar da zaɓe.

Dalilin kotu na ƙin amincewa da bukatar Atiku

Alƙalin ya amince da hujjojin lauyoyin Tinubu, APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), waɗanda suka nuna cewa amincewa da sababbin hujjojin zai sauya yanayin ƙarar tun farko.

A hukuncin da ya yanke kan bukatar gyara takardar ƙarar, Mai shari’a Ekwo ya ce Atiku yana neman maye gurbin hujjojin da aka gabatar tun farko da wasu sababbi. Ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulki.

Alƙalin ya kuma yi watsi da hujjar Atiku cewa gyaran da yake nema ba zai ƙara wasu sababbin batutuwa cikin ƙarar ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kotu ta soke tikitin takarar sanatan APC, ta ba tsohon gwamna nasara

Ya ce bayan nazarin bukatar a hankali, kotun ta gano cewa sabbin gyare-gyaren za su kawo wasu batutuwa da ba su cikin ƙarar tun farko.

A cewar alƙalin, amincewa da bukatar zai ba mai ƙara damar gabatar da sababbin hujjoji bayan wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada, tare da jawo rashin adalci ga waɗanda ake ƙara.

Hukuncin da alƙalin ya yanke

Mai shari’a Ekwo ya ce:

"Wannan ƙara tana da takamaiman wa’adi, kuma doka ta wajabta cewa dole ne a shigar da dukkan takardun shaida a kotu cikin kwanaki 14 daga ranar faruwar abin da ake ƙalubalanta.
“Duk wani abu da aka gabatar bayan kwanaki 14 ɗin da doka ta tanada ba shi da inganci ko wani tasiri a shari’a.
“Na gano cewa babu wani dalili mai ƙarfi a cikin wannan bukata ta gabatar da sababbin takardun shaida. Saboda haka, na ƙi amincewa da ita saboda ta saɓa wa tanadin doka.
“Na bayar da umarnin yin watsi da wannan bukata, kuma an yi watsi da ita.”

Kotun ta sanya ranar sauraron ƙarar

A wani mataki kuma, kotun ta sanya ranar 2 ga Disamba domin sauraron cikakkiyar ƙarar, bayan lauyoyin dukkan ɓangarorin sun amince da ranar.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; kotu ta dauki mataki kan matsalar auren Gwamna Abba

Atiku da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ne suka shigar da ƙarar a kan Tinubu, APC da INEC.

Masu ƙarar na neman kotu ta hana shugaban ƙasa da jam’iyyarsa shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, Atiku da ADC sun zargi APC da miƙa wa INEC takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC ta Tinubu wadda suka ce an ƙirƙira.

Sun nemi kotu ta umarci INEC ta cire sunan Tinubu da APC daga jerin ’yan takara da jam’iyyun siyasa da za su shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A ranar 10 ga Satumba, Atiku da ADC sun kuma shigar da wata takardar neman izinin gyara ƙarar da suka shigar tun farko.

Atiku ya kai Tinubu kotu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

ADC ta ce Atiku zai kifar da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta dage cewa Atiku Abubakar zai tsaya takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu da ya soke takararsa.

Jam’iyyar ta kuma yi iƙirarin cewa Atiku zai samu gagarumar nasara a zaɓen, duk da ƙalubalen shari’a da ya dabaibaye shugabancinta da shirye-shiryenta na zaɓen mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng