Kano: An Gano Gidan da aka Ajiye Mutane domin Safararsu zuwa Ketare

Kano: An Gano Gidan da aka Ajiye Mutane domin Safararsu zuwa Ketare

  • Hukumar NAPTIP ta reshen Kano ta karɓi mutane 10 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a unguwar Rijiyar Lemu
  • Wadanda aka ceto sun hada da mata da maza, inda ake zargin ana kan hanyarsu kai su kasar Libya domin bautar da su
  • Hukumar ta yaba wa ‘yan sandan Kano bisa namijin kokarinsu tare da jan hankalin iyaye a fadin Najeriya kan kare ‘ya ’yansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) ta karɓi mutane 10 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a Kano.

Shugaban hukumar reshen Kano, Abdullahi Babale ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da ya karɓi wadanda aka ceto daga hannun rundunar ‘yan sandan jihar.

Kara karanta wannan

An kama rikakken 'dan bindiga mai raba makamai a jihohin Arewa

Yan sanda
Yan sanda sun ceto mutanen da aka so safararsu zuwa Libya. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa an ceto mutanen ne a ranar 7 ga watan Disamba da misalin karfe 2:40 na rana a wani gida da ke Rijiyar Lemu a karkashin jagorancin CSP Bala Shuaibu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da aka ceto a jihar Kano

Rahotanni sun nuna cewa hukumar NAPTIP ta bayyana cewa wadanda aka ceto sun hada da mata 6 da maza 4.

An gano cewa ana kokarin kai mutanen kasar Libya ne domin bautar da su da kuma amfani da su wajen ayyukan da ba su dace ba.

Shugaban NAPTIP ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Salman Dogo-Garba, bisa goyon bayansa wajen ceto mutanen.

Za a mayar da wadanda aka ceto gidajensu

Abdullahi Babale ya ce za a ba mutanen shawarwari tare da lura da lafiyarsu sai kuma a mayar da su ga iyalansu.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su rika kula da ‘ya’yansu domin gujewa fadawa hannun masu safarar mutane.

Kara karanta wannan

An kama masu taimakon 'yan bindiga da kayan sojoji da 'yan sanda

Haka zalika, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya ja hankalin jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu da ya shafi safarar mutane domin daukar matakin gaggawa.

An kama mai safarar mutane a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta kama wani matashi a jihar Kano da ake zargi da safarar mutane zuwa ketare.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar da damke mutane 13 ana kokarin fita da su kasar Kamaru ta iyakar Najeriya a birnin Maiduguri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng