Disamba Ta Karato: Gwamna Ya Ware N50,000 ga Kowane Ma’aikaci a Jiharsa
- Gwamna Charles Soludo ya amince da biyan ma'aikatan gwamnatin Anambra ƙarin Naira 50,000 a matsayin kyautar ƙarshen shekara
- Za a saka kuɗin a cikin albashin watan Disamba na 2026 na dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar
- Gwamnan ya kuma amince da gyaran sakatariyar gwamnati, gina cibiyar fasahar sadarwa da kuma gyara hanyar sakatariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra — Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya amince da bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar kyautar Naira 50,000 a watan Disamba domin rage musu nauyin rayuwa.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a ranar Juma'a yayin bikin tunawa da Ranar Ma'aikatan Gwamnati ta shekarar 2026 da aka gudanar a Awka.
Soludo ya ce ya fahimci halin matsin tattalin arziki da ya shafi ikon sayen kayayyaki da sauran buƙatun jama'a, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan
Jita jita ta ƙare, an bayyana abin da aka tattauna tsakanin Peter Obi da 'yan Majalisar Amurka
Ya tabbatar da cewa dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar za su samu wannan kuɗi, kuma za a nuna shi kai tsaye a takardun albashinsu na watan Disamba na 2026.
Soludo ya yi magana kan biyan kyautar
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba ta ɗaukar alkawarin da ba za ta iya cikawa ba, yana mai cewa:
"Kafin mu ɗauki wani alkawari, muna tabbatar da cewa abu ne da za mu iya cikawa a kowane lokaci."
Ya kuma shawarci ma'aikata da su riƙa la'akari da kuɗaɗen shiga da albarkatun da kowace jiha ke da su kafin yin kwatancen albashi tsakanin jihohi.
A cewarsa, gwamnatinsa na fifita shugabanci mai ɗorewa maimakon yin alkawuran da ba su da tushe.
Gwamna ya amince da gyaran sakatariya
Baya ga kyautar kuɗin, Soludo ya amince da wasu ayyukan inganta muhallin aiki da kayayyakin more rayuwa a sakatariyar gwamnatin jihar.
Ayyukan sun haɗa da zamanantar da muhallin sakatariya, kafa cibiyar fasahar sadarwa da kuma gyaran hanyar sakatariyar, cewar Punch.
Gwamnan ya kuma gode wa ma'aikatan bisa goyon bayan da suka ba gwamnatinsa a lokacin zaɓen gwamna, yana mai cewa yana da yakinin yawancinsu sun zaɓe shi saboda ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke gudanarwa.
Shugabar ma'aikata ta yaba da dawo da tsaro
A jawabin maraba, shugabar ma'aikatan gwamnatin jihar, Ngozi Iwouno, ta yabawa Soludo bisa ƙoƙarin dawo da tsaro da zaman lafiya a sassa daban-daban na Anambra.
Ta ce ma'aikatan gwamnati yanzu suna zuwa wuraren aikinsu akai-akai kuma a kan lokaci, saboda fargabar zaman gida na ranar Litinin ta ƙare.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng
