Masu Garkuwa Da Mutane
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Taraba kan dira kan wasu 'yan bindiga da suka sace mutane. Sun kubutar da mutanen da miyagun suka sace.
Yan sanda sun kai farmaki a jihohi inda aka ceto mutane sama da 30. An ceto mutane 20 a Katsina tare da kama shugaban masu garkuwa Idris Alhaji Jaoji.
Ana fargabar 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata sabuwar amarya da kawayenta hudu a jihar Sokoto. An ce 'yan bindigar masu biyayya ne ga Bello Turji.
yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kashe yan bindiga uku cikin wadanda suka sace daraktan ma'aikatar shari'a suka daure shi a cikin wani rami da 'yar uwarsa.
Yan sanda a Katsina sun kama wani rikakken dan damfara da ke satar ATM yana cire kudin mutane. An kama matashin da ya sace matar aure a jihar Katsina.
Wani matashin mai tsaron gona ya yi karfin hali. Sule Gende ya hada kai da abokansa don a sace shi. Ya nemi a biyasu miliyoyin Naira a matsayin fansa.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace kansila da wasu mutane 8 a jihar Kogi. Yan bindigar sun bi gida gida ne suna garkuwa da mutane a yankin.
'Yan bindiga sun kashe fasto a Kwara yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jana'iza. Sun yi garkuwa da wasu mutum uku kuma suna neman Naira miliyan 30 kudin fansa.
An samu budurwa mai shekaru 19 tsirara bayan masu tsafi sun sace ta a Kwara. Budurwar na karatu a jami'ar jihar Kogi kuma NSCDC na shirin mayar da ita gida.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari